Jagoran APC kuma wanda ke sahun gaba wajen ganin APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Bola Tinubu, ya gana da Sanatocin APC, inda ya nemi goyon bayan su domin ya samu nasarar tsayawa takara, kuma ya lashe zaɓen 2023.
Tinubu ya isa Majalisar Dattawa wajen ƙarfe 3 na yamma a ranar Laraba, inda ya gana da Sanatocin APC, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da sauran masu riƙe da muƙamai na APC na Majalisar Dattawa.
Tinubu ya kai masu ziyarar mai kama da kamfen, makonni biyu kafin taron gangamin APC, wanda za a zaɓi shugabannin jam’iyya.
Tun cikin watan Janairu ne TInubu ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari aniyar sa ta neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Tinubu ya shaida wa dattawan Sanatocin APC cewa ga fa zaɓe ya gabato, amma fa ba shi iya yin kamfen shi kaɗai.
Ya ce dalili kenan ya ke nema da buƙatar goyon bayan su domin su taimaka ya cika burin sa na zama shugaban ƙasa.
Ya roƙi su taimaka ya ci zaɓen fidda-gwanin APC domin ya gaji Shugaba Buhari.
Ya ce ganin yadda ya yi gwamna tsawon shekaru takwas a Legas da kuma kasancewa ya taɓa yin kamata, to ya cancanci zama shugaban ƙasa.
Cikin watan Fabrairu ne Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya ce Tinubu kaɗai ke da ‘laƙanin’ iya gyaran Najeriya.
A labarin, Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya nuna cewa jagoran APC Bola Tinubu kaɗai ya ke goyon baya a cikin masu takardar neman tsaya wa APC zaɓen 2023.
A ranar Juma’a ce ya bayyana cewa Tinubu wanda shi ma ya taɓa yin gwamna na jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, shi kaɗai ne a cikin masu neman tsayawa takara ke da abin da ya kira “laƙanin iya gyara Najeriya”.
Da ya ke magana a wurin taron haɗa-ka na Kwamishinoni da ‘Yan Majalisar Jihar Lagos, Sanwo-Olu ya ce Tinubu ya na da dukkan wasu sabubban cancantar ya mulki Najeriya, kuma idan ya zama shugaba, ko shakka babu zai iya maida ƙasa tsaba.
“Ya kamata mu tafi tare, musamman ganin yadda zaɓen 2019 ya gabato. Ina yin kira a gare mu baki ɗaya mu taru mu haɗa kai mu goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen fidda-gwani na APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
“Ya yi wa al’ummar Jihar Legas dukkan wani abin da zai iya yi. To a yanzu ya na so ya yi wa Najeriya gyara kamar yadda ya gyara Legas ta samu gagarimin ci gaba.
“Tinubu ne mutumin da ya fi cancanta ya mulki Najeriya. Saboda ya san matsalolin da su ka addabi ƙasar nan sosai, kamar yadda yadda ya san bayan hannun sa. Kuma ya na da laƙanin da zai yi amfani da shi ya yi gyaran Najeriya.” Inji Sanwo-Olu.
Sanwo-Olu dai shi ne Tinubu ya bai wa takarar gwamnan Legas a zaɓen 2019, bayan ya hana gwamnan lokacin, Akinwunmi Ambode tsayawa takara karo na biyu, domin ya yi tazarce.
Bisa dukkan alamu Tinubu na iya samun tirjiya daga jihohin Kudu maso Yamma, ganin yadda wasu suka tashi haiƙan dare da rana su na buga wa Matakimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo gangar ya fito takara shi ma.
Discussion about this post