Peter Obi, mataimakin shugaban kasa na takarar Atiku Abubakar a zaɓen 2019, ya ƙaddamar da fitowa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023.
Ya ƙaddamar da takarar mako guda bayan da Atiku Abubakar ya ƙaddamar da ta sa takarar.
Obi ya ƙaddamar a ranar Alhamis a Awka, inda ya yi wa al’ummar yankuna 181 jawabai a Gidan Gwamnatin jihar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
“Na zo nan domin na sanar da ku aniya ta ta neman fitowa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023. Kuma ina buƙatar goyon bayan ku.”
Haka Obi ya shaida wa sarakunan waɗannan yankuna 181.
“Bayan na yi dogon nazari, na fahimci Najeriya a rarrabe ta ke. Saboda haka na yi alƙawarin zan ɗinke ɓarakar Najeriya, kuma zan samar wa Najeriya ɗimbin masu zuba jari.
“Najeriyar da zan jagoranta za ta samu ɗimbin aiki ga ‘yan ƙasar. Za a bunƙasa tattalin arziki, ilmin zamani. Ina da dama da nasibin da inganta tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai bunƙasa.”
“Na ciyar da Najeriya gaba daga ƙasa wadda ta fi maida hankali wajen narkar abinci zuwa ƙasa wadda ke sarrafa kayayyaki ta na fitarwa waje. A matsayi na na ɗan Najeriya, zan samar da tsaro a ƙasar nan. Ni ba matsayin mulki na siyasa na ke nema ba. Ina so ne na zama bawan ‘yan Najeriya na bauta masu.”
Peter Obi ya fito takara a makon da dattawan Kudu maso Kudu su ka ce tilas fa sai ɗan Kudu zai zama shugaban ƙasa -Dattawan Kudu-maso-kudu, ‘yan PDP.
Shugabannin PDP na Reshen Kudu maso Kudu, sun ce babu ruwan su da wani ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP daga Arewa, su sai fa ɗan kudu ne kaɗai su ka amince ya yi shugabanci a zaɓen 2023.
Wannan buƙata ta su na cikin wata sanarwar bayan taro da su ka fitar na shugabannin PDP na yankin Jihohin Ƙabilun Kudu maso Kudu. Sun yi wannan taro ne ranar Litinin a Uyo.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Kudu kuma Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shi da Gwamna Nysom Wike na Ribas har ma da Udom Emmanuel na Akwa Ibom duk sun halarci taron. Haka ma Gwamna Douye Diri na Bayelsa, shi ma ya halarta.
“Wannan Shiyya ta Kudu maso Kudu na goyon bayan matsayar Gwamnonin Kudu cewa sai fa ɗan Kudu ne zai yi shugaban ƙasa a zaɓen 2023.” Haka dai shugabannin su ka ƙara jaddadawa.
Gwamna Okowa ya ce jam’iyyar PDP na da “ƙudirin da ta ke son ta cimma” na ceto Najeriya daga jam’iyyar APC. Sannan kuma ya yi kira ga PDP ta kasance cikin haɗin kai domin a ci gaba da tafiya tare daga nan har zaɓen 2023.
“Mun yi amanna cewa nan da watan Fabrairu 2023, za mu samu gagarimar nasarar lashe zaɓe, mu ceto Najeriya.”
Haka ya furta a wurin taron wanda mambobin Majalisar Tarayya na Kudu Maso Kudu suka halarta tare da shugabannin PDP na shiyya.
Shi kuwa Gwamna Wike cewa ya yi PDP a yanzu ta na da damar karɓe mulki ta hanyar zaɓe daga hannun APC. Don haka ya ja hankalin cewa kada a yi wasa ko wasarere da wannan dama ta suɓuce.
“Yan Najeriya na jiran PDP ta amshi mulki kawai a zaɓen 2023. Amma fa hakan ba zai yiwu ba idan ba mu haɗa kan mu ba, kuma mun yi aiki tare.”
Gwamna Emmanuel cewa ya yi PDP cewa ya yi jam’iyyar PDP ce kaɗai ke iya farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan daga halin ƙuncin da ‘yan ƙasar ke fama da shi da kuma gurguntakar tattalin arziki.
Daga nan shugabannin PDP sun nuna damuwa kan yadda har yanzu Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC) har yanzu ta ke a hannun Kantoman Riƙo. Daga nan su ka ce wannan an karya dokar NDDC, kuma su ka nemi a kafa Hukumar Gudanarwar NDDC ba tare da ci gaba da ɓata lokaci ba.
A ƙarshe sun kuma nemi a fito da sakamakon binciken badaƙalar cin kuɗaɗen NDDC domin kowa ya gani.