Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana matsayin jam’iyya dangane da bin tsarin karɓa-karɓa wajen zaɓen shugabannin jam’iyya da masu mukamai siyasa.
Yayin da PDP ta yi nasarar tsallake batun raba muƙaman shugabannin jam’iyya bisa tsarin shiyya-shiyya a gangamin PDP na 2021, har yau ba ta samu damar warware matsalar ko daga inda ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito ba na zaɓen 2023.
Manyan PDP daga yankin Arewa na ta kiraye-kirayen a yi watsi da batun karɓa-karɓa ko shiyyanci, ba bar ko ma ɗan wane yanki ya fito takara a yi zaɓen fidda gwani kawai.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na a sahun gaban masu neman fitowa takara a PDP, kuma tuni ya ke yin kira cewa a wancakalar da batun karɓa-karɓa tsakanin masu takara. Ya na so ko ma ɗan wane yanki ya fito kawai.
Haka shi ma Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya bayyana a ranar Talata, tare da yin jan hankalin cewa a fitar da wanda ya cancanta, ko ma daga ina ya ke, ba sai lallai daga wata shiyya ba.
Sai dai su kuma Gwamnoni da Shugabannin PDP na Yankin Kudu maso Kudu sun ce lallai sai ɗan kudu ne za a bai wa takara, kuma shi zai yi mulki a 2023.
Shi kuwa Shi cewa ya yi, “duk ɗan takarar da a yanzu ya ke jin idan an yi tsarin karɓa-karɓa ba zai iya fitowa daga yankin sa ba, to ya jira sai zaɓe na gaba sannan ya jaraba sa’a.
“Jam’iyyar PDP na da tarihin bin tsarin karɓa-karɓa na shugabannin jam’iyya da muƙaman siyasa. Duk wanda ba yankin sa mai neman takara zai fito, to ya jira sai zaɓen shugaban ƙasa na gaba, sai ya jira zaɓe na gaba.”
“Mu na da yaƙini da tabbacin cewa PDP za ta lashe zaɓen 2023. A wannan lokacin za mu tabbatar cewa ta kewaya kowane yanki a cikin adalci, gaskiya ba tare da kaucewa abu mafi alheri ga Najeriya.”
Kwamitin Rarraba Muƙamai a Tsakanin Shiyya-shiyya na PDP dai an ba shi umarnin ya bayar da jerin sunayen yadda za a yi rabon muƙamai a bisa tsarin shiyya shiga, nan da ranar 30 Ga Maris.