Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana cewa sai mutumin ƙwarai, sahihi ya kamata ya shugabanci Najeriya a 2023, ba rubabi-rubabi ba.
Gowon ya furta haka ne a ranar Juma’a, lokacin da ƙungiyar Tallata Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ta kai masa ziyara a gidan sa da ke Asokoro, Abuja.
Ƙungiyar mai suna Progressive Consolidated Group, sun Kai masa ziyarar ce domin su sanar da shi aniyar su ta ganin cewa zaɓen Osinbajo shi ne mafita kuwa hanyar fidda Najeriya daga ƙuncin da ‘yan ƙasar ke ciki.
Gowon ya ce duk da ba ya yin katsalandan cikin harkokin siyasa, amma bai ba zai ƙi yi wa ‘yan Najeriya nasiha ba cewa wajibin dukkan kowa da kowa ne su ga cewa sun haɗa kai an samu ci gaba, zaman lafiya da shugabanni nagari daga sama har ƙasa.
Yayin da Gowon ke bayani, ya ce ya kamata a sani cewa duk sharri da tuggu da ƙulle-ƙullen da za a yi don a hana wani nasara, to Ubangiji ne ke ƙaddara wanda zai yi mulki.
Ya kuma ja hankulan masu kafafen yaɗa labarai su fi maida hankali wajen tabbatar da haɗin kan ƙasar nan.
Sannan kuma ya ce ba za a kai gaci ba har dai masu neman muƙamai wato ‘yan siyasa sun cusa kishi su da magoya bayan su, maimakon a riƙa ɗin bada ƙarfi wajen neman muƙamai wurjanjan.
Tawagar da ta kai wa Gowon ziyasa na ƙarƙashin Baraden Lafiya, Musa Kwande da Babban Kodinetan PCG, Ahmed Kari.
Bayan yin jawabai sun kuma gana asirce da Gowon.
Yayin da guguwar neman shugabancin Najeriya ta fara turnuƙun yaƙi tun ana shekara ɗaya kafin zaɓe, ɗan neman takara a ƙarƙashin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal, ya ce kada a zaɓi wanda ya cimma shekaru 60 a zaɓen shugaban ƙasa.
Gwamna Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto da ke neman a tsaida shi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, ya gargaɗi ‘yan Najeriya cewa kada a yi saki-na-dafen sake zaɓen dattijon duk da ya cimma shekaru 60 abin da ya yi sama a matsayin shugaban ƙasa, a zaɓen 2023.
A yanzu dai Tambuwal shekarun sa 56 da haihuwa, kuma ya dage bakin ƙoƙarin sa ya na son ganin cewa PDP shi ta tsayar, ba Atiku Abubakar ko wani ba.
Tambuwal ya yi wannan bayani a Jihar Jigawa, bayan da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) na Jihohin Arewa 19 su ka yi masa mubaya’a, su ka ce shi ne ɗan takarar su.
Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Sokoto, Bashir Usman ne ya wakilci Tambuwal a taron.
“Matasan Najeriya su ke da ƙasar nan. Duk wanda ya haura shekaru 60 a duniya, shure-shuren ƙarasawa ya tarad da mahaliccin sa kawai ya ke yi amma ba motsa jikin ƙarin ƙarfin iya shugabancin ƙasa ya ke ba.” Inji Tambuwal a wurin taron.
“Mu na buƙatar shugaban ƙasar mai lafiya ƙalau. Mai ƙarfi gagau, mai kuzari garau. Kuma mai jimirin kazar-kazar da gwarin-guiwar jure gaganiyar shugabancin al’umma kamar Najeriya.
“Mu na buƙatar lafiyayyen shugaba wanda zai iya kewaye Najeriya ɗaya rana domin ya gani kuma ya ji dukkan abubuwan da ke faruwa ko su ke addabar ‘yan Najeriya. Amma ba wanda kawai zai zauna cikin ofis ya na shan iska ya na jiran a kawo masa rahotonnin da aka daddatse, aka cire wuraren da su ka kamata ya ji ba.”
Tambuwal kuma ya ce kada a zaɓi duk wanda aka san ya na fama da wata rashin lafiya wadda ya same ta ne saboda yawancin shekaru.