Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ce sabbin shugabannin APC a yanzu dai ba su ware wani yanki ko shiyya da suka ce sai daga can ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito ba. Kuma ba su ware wasu shiyyoyi suka ce kada su nemi takarar shugabancin Najeriya ba.
Bello ya yi wannan jawabi a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai Onogwu Mohammed ya fitar a ranar Litinin, a Abuja.
Gwamnan ya ƙara da cewa ya na da yaƙini a zaɓen 2023 sai APC ta samu aƙalla ƙuri’u miliyan 41, matsawar dai aka fitar da ɗan takarar da jama’a shi suka fi amincewa da shi.
Ya jaddada cewa zaɓen da aka yi wa Abdullahi Adamu ya zama Shugaban APC na Ƙasa ba zai zama barazana, tarnaƙi, dabaibayi ko wani shingen da shi gwamnan zai kasa tsallakewa ya fito takarar shugaban ƙasa ba.
Gwamna Yahaya Bello da Abdullahi Adamu sun fito ne daya Shiyyar Arewa ta Tsakiya, wato daga jihohin Nasarawa da Kogi.
Ana ganin cewa babu yadda za a yi jam’iyya ta fitar da ɗan takarar shugabancin ƙasa a shiyya ɗaya da shugaban jam’iyya.
Sai dai kuma Yahaya Bello ya ce wannan duk ba wani abin dogaro ba ne. Ya ce idan APC na so ta yi gagarimar nasara, to ta tsayar da wanda zai iya kawo mata nasara, wanda mutane ke so kuma wancan ya cancanta.
Ya ce kasancewar Adamu Shugaban APC na Ƙasa, hakan gagarimar nasara ce, domin zai ɗinke duk wata ɓaraka, tunda shi jama’a ke so dama ya shugabanci jam’iyya.
Yahaya Bello ya yi alƙawarin idan ya zama shugaban ƙasa zai ƙara samar wa mata muƙamai a gwamnatin sa.
Cikin watan Fabrairu ne a Fadar Shugaban Ƙasa Yahaya Bello ya ce ‘Yankin Arewa ta Tsakiya ya cancanci shugabancin Najeriya’.
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi masa bayanin halin matsalar tsaro da jihar ke ciki.
Da ya ke bayani ga manema labarai bayan ganawar sa da Buhari a keɓance, Yahaya Bello ya ce masu jihar Kogi an samu zaman lafiya, sanadiyyar tsauraran matakan tsaron da gwamnatin jihar ta ɗauka.
Gwamnan ya ce ‘yan Najeriya baki ɗaya na da rawar da kowa zai taka wajen tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan su tashi tsaye zama wasu ejan-ejan masu kai wa jami’an tsaro wajen tona asirin miyagun mutane, domin a samu sauƙin samar ta ingantaccen tsaro a ƙasar nan.
“Na kawo wa Shugaban Ƙasa ziyara ce kamar yadda na saba, don na sanar da shi irin ci gaban da aka samu wajen samar da tsaro a Jihar Kogi.
“Kamar yadda ku ka sani, a lokacin da na hau mulki, Jihar Kogi ce ta fi sauran jihohin ƙasar nan rashin tsaro.
“Amma a yau da taimakon Allah, Jihar Kogi ce ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya.
“Kuma Shugaban Ƙasa ya yi matuƙar murna da farin cikin irin waɗannan bayanai da na yi masa, tare da ci gaban da jihar ta samu a ɓangaren tsaro, tattalin arziki, samar da ayyukan bunƙasa harkokin rayuwa na yau da kullum, zaman lafiya da haɗin kai, duk sun wanzu a Jihar Kogi.
“To waɗannan bayanai dai su ne ainihin abin da mu ka tattauna da Shugaban Ƙasa. Kuma ya ce na isar masa da gaisuwa da fatan alheri ga ɗaukacin al’ummar Jihar Kogi.”
Bello ya ce gwamnatin Buhari ya yi gagarimin aiki sosai a fannin inganta tsaro.
Sai dai kuma ya yi ƙorafin cewa kafafen watsa labarai ba su yayata nasarorin da aka samu a fannin tsaro. Ya ce bba wani abu ba ne siyasa ce.
Batun Takarar Yahaya Bello 2023:
Dangane da yiwuwar ɗan takarar APC a Zaɓen 2023 ya fito daga Arewa ta Tsakiya, Gwamna Bello ya bayyana Arewa ta Tsakiya cewa yankin ne aka fi dannewa fiye da sauran dukkan yankunan Najeriya, tun bayan samun ‘yanci a 1960.
A kan haka ne ya ce a zaɓen 2023, yankin Arewa ta Tsakiya ne ya fi dacewa da cancanta.
Bello ya yi maganar ce an matsayin raddi ga shugabannin Ohanaeze Ndi Igbo, masu cewa Yankin Kudu maso Gabas ne ya fi dacewa ya yi mulkin Najeriya a 2023.
Gwamna Yahaya Bello dai ya fi sauran dukkan masu sha’awar fitowa takara nuna maitar sa ta neman shugabancin ƙasa a fili.