Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kama ‘yan bindiga 10, an kashe mutum daya, an fatattaki wasu ‘yan bindigan sannan dakaru sun ceto mutum daya da aka yi garkuwa da shi yana tsare a hannun su.
Kakakin rundunar Mohammed Shehu ya ce ‘yan sandan sun samu wannan nasara ne a dalilin tsauraran matakan gamawa da ‘yan bindiga da suka dauka.
Shehu ya ce ‘yan sandan sun kama wani shahararren dan bindigamai suna Lawali Ruguduma a karamar hukumar Bukkuyum, jami’an tsaron sun kashe dan bindiga daya a lokacin da suke batakashi da ‘yan bindiga a Kwarin Ganuwa da Nasarawar Mai Fara sannan suka kama manyan bindigogi biy kirar AK-47.
Ya ce ‘yan sandan sun kama ‘yan bindiga 8 sannan sun ceto wata mata mai shekaru 60 da aka yi garkuwa da ita a karamar hukumar Gumi.
“Yan bindigan da aka kama sun hada da wani mai suna Umaru Alhaji – Abdu, Buban Buba da Abubakar Shehu,
Sanna kuma akwai Abdullahi Sangamere, Sidi Masallaci, Mohammed Ajiya, Saminu Bala da Muhammad Sani. Bayan haka sun tabbatar wa jami’an tsaro cewa sune suka buwayi mutane a karamar hukumar Gumi.
Shehu ya yi Kira ga jama’an jihar da su hada hannu da jami’an tsaro domin ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a jihar. Ya kuma hore su da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun Karin zaman lafiya a jihar da Najeriya baki daya.
Shehu ya tabbatar cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar ba.