An samu ragowa a yawan mutanen da ‘yan bindiga ke kashewa a kasar nan. A makon jiya wanda daga ranar 27 Fabrairu zuwa 5 ga Maris 2022 mutum 10 ne aka kashe a kasar nan.
A cikin mutum 10 din da aka kashe akwai mutum biyu da mutane suka babbake saboda sun saci wayar salula sannan da mutum 8 da ‘yan bindiga suka kashe a jihar Zamfara.
A wancan mako mutum 62 ne ‘yan bindiga suka kashe a kasar nan.
Idan ba a manta PREMIUM TIMES tun a watan Nuwanba 2021 ne take bada rahotan adadin yawan mutanen da ‘yan bindiga ke kashewa.
Rahotan da gidan jaridar ke badawa daga wadanda gidajen jaridu suke rawaitowa ne a cikin mako daya.
Jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun kashe mutum 8 a jihar Zamfara daga cikin mutum 10 da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Zurmi.
‘Yan bindigan sun yi garkuwa da mutum 10 a ranar 1 ga Satumba 2021 saboda sun yi kokarin kai wa hedikwatan karamar hukumar hari.
Maharan sun kashe mutane saboda ‘yan uwan su sun ƙasa biyan Naira miliyan 6 da suka bukata.
Jihar Anambra
A ranar Laraban da ya gabata ne mutane suka banka wa wasu mutum biyu wuta bayan an kama su da laifin sace wa wata mata wayar salula da wasu kaya a Onitsha jihar Anambra.
Mutanen da abin ya faru a idonsusun ce sai da aka yi wa barayin duka sannan aka rataya musu taya Kuma aka duldula mutu fetur Kuma aka kesta ashana.
Kashe ‘yan bindiga
Babu wanda ke da masaniya ko raguwan da aka samu a hare-hare da kisan da ‘yan bindiga ke yi na da alaka da alkawarin gamawa da ‘yan bindiga da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi a kwanaki baya.
Daga daga cikin alkawarin da shugaban Buhari ya dauka ya faru ranar 5 ga Janairu bayan ‘yan bindiga da suka kashe mutum sama da 200 tare da cina wa gidaje da dama wuta a kauyukan dake kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.
Buhari ya yi tir da kisan mutanen da ‘yan bindigan suka yi sannan ya tabbatar cewa zai aika da dakarun sojin zama da ƙasa domin ganin an kare mutane a jihsr Zamfara.
Rahotanin sun nuna cewa a cikin kwanaki nan ‘yan bindiga basu kashe kowa ba a jihar Zamfara ba.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta bada rahoton yadda ‘yan bindiga a cikin makonni uku a shekaran 2022 suka kashe mutum sama da 200 a jihar Zamfara sannan a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa ta kashe ‘yan sama da 200 a jihar Neja.
Hada hannu da jami’an tsaro
A taron AANDEC da aka yi shugaban ƙasa Buhari ya yi Kira ga mutane da su hada hannu da jami’an tsaro domin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.
Ya ce za a samu nasara idan matuka idan mutane suka hada hannu da jami’an tsaro.
Discussion about this post