Yan bindiga sun Kashe mutum 103 a Najeriya a cikin makon da ya gabata kamar yadda alakluman kididdiga suka nuna.
Daga cikin mutum 103 din da aka kashe akwai jami’an tsaro 24 da suka hada da sojoji 18, ‘yan sanda 6 farin hula 79.
Tsakanin wancan mako da makon da ya gabata Najeriya ta samu karin kashi 900% da aka kashe a kasar nan.
Mafi yawan kisan mutanen da aka yi a makon da ya gabata sun auku ne a jihar Kebbi da wasu jihohi biyu.
Jihar Kaduna
‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu sannan sun yi garkuwa da fasto cocin darikar katolika Joseph Akeke dake kauyen Kudendan.
‘Yan bindigan sun afka kauyen da misalin karfe 1 na safiyar Talatan makon jiya.
Jihar Kebbi
Akalla ‘yan sa kai mutum 63 ‘yan bindiga suka kashe ranar Lahadin da ya gabata a jihar Kebbi.
Wasu sarakunan gargajiya a jihar sun bayyana wa BBC Hausa cewa ‘yan sa kan sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke bin wasu ‘yan bindiga da suka kawo wa kauyukan su hari inda a dalilin haka Suka fada tarkon da ‘yan bindigan suka dana musu.
A karamar hukumar Sakaba wasu mutum biyu mazauna kauyen da basu so a fadi sunayen su sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa adadin yawan ‘yan sa kan da aka kashe ya fi yawan da ake fadi.
Jihar Katsina
Akalla yara 7 ne suka rasa rayukansu yayin da mutane ke tsere wa harin ‘yan bindiga a kauyen Shimfida dake karamar hukumar Jibia.
Hakan ya faru bayan cire sojoji da aka yi daga kauyen ranar Alhamis din da ya gabata.
Daga nan wasu fasinjoji mutum biyar sun mutu mutum uku sun ji rauni a yayin da ‘yan bindiga suka kuba wa motar su wuta a hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Dan Musa ranar Asabar da safe.
Dan Musa na daga cikin kananan hukumomin dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga domin wurin na da iyakan ƙasa da dajin Rugu da kauyukan Safana, Kankara da jihar Zamfara.
Jihar Ogun
A ranar Litinin din ya gabata ‘yan bindiga sun banka wa sarkin Olowe Gbagura Akin Muheedeen wuta a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa
‘yan bindigan sun kashe basaraken yayin da yake hanyar dawowa daga sallar Asuba.
Discussion about this post