Mai Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Chelsea da ke Landan, babban birnin Ingila, ya fitar da sanarwar cewa ya saka ƙungiyar a kasuwa, zai sayar da ita.
Sayarwar dai ta biyo bayan siyasar da ta shiga ne a Rasha, Ingila da duniya dangane da farmakin da Rasha ke ci gaba da kai wa Ukraniya.
Ana zargin Abramobich mai Chelsea na da kusanci na ƙut-da-ƙut da Shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Tun a kwanan baya da Abramobich ya miƙa ragamar riƙon Chelsea ga wata gidauniyar tallafa wa jama’a. Amma a ranar Laraba ya fito ya yi sanarwar cewa daga yanzu ƙungiyar na kasuwa, zai sayar da ita.
Ya ce ya ɗauki wannan shawara domin hakan ce mafi alheri a gare shi, ga kulob ɗin, magoya bayan kulob ɗin da masu bada tallolin ɗaukar nauyin kulob.
A cikin shekaru 19 da Abramobich ya sayi Chelsea, ya kashe wa kulob ɗin fiye da fam biliyan 1, sannan kuma kulob ɗin ya lashe manyan kofukan gasanni har 19.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda FIFA da UEFA su ka dakatar da ƙungiyoyin Rasha daga buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya.
Siyasar yaƙi ta keta cikin wasan ƙwallon ƙafa, inda Ƙungiyar Shirya Wasannin Ƙwallo ta Duniya (FIFA) da Kungiyar Shirya Wasannin Ƙwallon Turai UEFA suka sanar da dakatar da Rasha daga shiga kowace gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.
Haka nan kuma an dakatar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar Rasha daga buga wasannin Champions League da na UEFA da UEROPA.
Ƙungiyar Ƙwallon Turai ta ƙunshi ƙasashe 55 na Turai, kuma a ranar Litinin UEFA da FIFA su ka yi wannan sanarwa cewa sun dakatar da ƙungiyoyin da ke buga wa ƙasar Rasha kuma sun dakatar da kulob-kulob na ƙungiyoyi daban-daban har sai yadda hali ya yi.
Da farko dai ba dakatar da Rasha aka yi ba. Sanarwa aka yi cewa ƙungiyoyi daga wasu ƙasashe su daina zuwa Rasha wasa. Duk wasan da za a yi a Rasha, to a yi shi a wata ƙasa can da ba ta goyon bayan Rasha ko Ukraniya.
Sannan kuma aka ce ba za a bar ‘yan kallo ko mutum ɗaya ya shiga filin wasa ba. Kuma an haramta yin taken ƙasar Rasha da filfila tutar ƙasar a filin wasan.
Daga baya kuma sai UEFA da FIFA suka yanke shawarar dakatar da Rasha ɗin baki ɗaya.
A ranar Lahadi PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Rasha ta yi ramuwar gayyar ƙwace kadarori da kuɗaɗen kamfanonin Amurka da na Ƙasashen Tarayyar Turai da ke ƙasar ta.
A wani kakkausan matakin da Rasha ta ɗauka a ranar Asabar, ta maida raddin ƙwace dukiyar ƙasar da Amurka da Tarayyar Turai suka yi, inda ita ma ta bayyana ƙwace na su kuɗaɗen da tulin dukiyoyin da ke Rasha.
Mataimakin Shugaban Majalisar Tsaron Rasha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Rasha (RIA) cewa su ma za su ƙwace ilahirin kadarorin duk wani kamfanin Amurka da ke Rasha da kuɗaɗen da kamfanin ya malkaka.
Sannan kuma za ta ƙwace dukkan kuɗaɗen wani Ba’Amurke da ke Rasha da illahirin kadarorin sa.
Wannan mataki ya faɗa kan duk wani kamfanin ƙasashen Turai da ke cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da na duk wata ƙasa mai goyon bayan Ukraniya.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Amurka da Birtaniya sun ƙwace ilahirin dukiyar Rasha da ke ƙasashen su.
Firayi Ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana tsauraran matakan karya tattalin arziki da ƙasar ta ɗauka a kan Rasha, sakamakon mamaye Ukraniya da Rasha ta yi a ranar Alhamis.
Ya ce Birtaniya tare da amincewar Majalisar ƙasar, ta ƙwace kuɗaɗen manyan bankunan Rasha da ke cikin ƙasar, sannan kuma ta haramta dukiyoyin manyan kamfanonin Rasha da ke ƙasar.
Daga cikin takunkumin akwai kuma haramcin hana manyan kamfanonin Rasha hada-hadar kuɗaɗe, saye ko sayar da kaya a Birtaniya.
An kuma haramta wa duk wani kamfani ko banki na Birtaniya bayar da bashi ga kamfanonin Rasha.
Takunkumin ya shafi wasu manyan kamfanonin Rasha, har da wani kamfani mafi girma da ke shirin ɗaukar ma’aikata miliyan biyu.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Amurka, Tarayyar Turai da G7 su ka ƙaƙaba takunkumi 8 don karya tattalin arzikin Gwamnatin Putin.
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa Amurka ta ƙwace ilahirin dala tiriliyan 1 mallakin wasu manyan bankunan Rasha 4, waɗanda bankunan ke hada-hada da su a Amurka.
Wannan mataki na ɗaya daga cikin matakan da Amurka ta ɗauka domin ɗanɗana wa Rasha gayyar laifin afka wa Ukraniya da yaƙi da Shugaban Rasha Putin ya yi.
Yayin da Biden ke jawabi a ranar Alhamis, ya ce sun tattauna da Tarayyar Turai wadda ƙungiya ce mai mambobin ƙasashe 27, da kuma mashahuran ƙasashe masu arziki bakwai na duniya, wato G7, su ma duk za su ɗauki matakan ƙwace ilahirin kuɗaɗen bankunan Rasha da ke ƙasashen su.
Biden ya ce za a ɗauki waɗannan tsauraran matakai ne domin a gurgunta tattalin arzikin Rasha, ta yadda al’ummar ƙasar za su ɗanɗana abin da shugaban su ya janyo masu.
Sauran matakan sun haɗa da toshe wasu kafafen hada-hadar kasuwancin Rasha a Amurka da Turai, daina cinikayya da hana Rasha sayar da kayan ta a Amurka da Turai da kuma hana manyan kamfanoni da bankunan ƙasar da manyan ‘yan kasuwar ta yin duk wata hada-hada da neman bashi a Turai da Amurka.
Yayin da Ƙungiyar Ƙasashen Afrika (AU) ta yi tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraniya, tuni Birtaniya ta bi sahun Amurka, ta ƙaƙaba wa Rasha tsauraran matakai.