Ƙasar Faransa ta bada sanarwar ƙwace kadarorin manyan hamshaƙan Rasha da aka ƙiyasta sun kai fan miliyan 850, kwatankwacin Euros miliyan 938.
Ministan Harkokin Tattalin Arzikin Faransa, Bruno ne ya ce an ƙwace kadarori na fan miliyan 539.
Ya ce akwai wasu attajiran Rasha masu ajiyar jimillar Euro 150 a bankunan Faransa daban-daban, su ma an ƙwace su. An kuma ƙwace wasu jiragen ruwan manyan attajiran Rasha na kimanin Euro miliyan 150.
Faransa dai ta kafa kwamitin ƙwace kadarorin manyan ‘yan kasuwar Rasha da kuma hamshaƙan da ke da kusanci da Shugaba Vladimir Putin.
Wannan jarida ta bada rahoton yadda Ukraniya ta yi fatali da buƙatar Rasha na ta yi sarandar birnin Mariupol.
Ukraniya ta ƙi yarda da umarnin Rasha na dakarun ta su ajiye makamai su yi saranda a birnin Mariupol, birnin mai arzikin tashoshin ruwa a rasha.
Rasha ta ce mafi alheri ga dakarun Ukraniya shi ne su ajiye makamai, domin ta bar su su fice daga birnin ko kuma dakarun Rasha su yi masu kirɓin-sakwarar-mahaukaciya.
“Babu wata maganar mun amince da yin saranda. Kuma dakarun Ukraniya ba za su ajiye makamai ba. Mun kuma rigaya mun shaida wa mahukuntan Rasha hakan.”
Mataimakin Firayi Ministan Ukraniya, Irina Vereshchuk ya shaida wa jaridar Ukrainska Prava.
A cikin wani faifan bidiyo da aka nuno ta, Vereshchuk ta ce dakarun Rasha na nuna hali a aikata halaye irin na ‘yan ta’adda.
“Sun cika magana su na tubƙa da warwara. Da safe sun ce sun haƙura da kai hari. Da yamma kuma sun ci gaba da yi wa garin ruwan wuta.
“Maimakon a tsaya ɓata lokacin rubuta wasiƙa mai ɗauke da shafuka takwas, su buɗe hanya mana kawai a fice daga birnin.*
Magajin Garin Mariupol Piotr Andryushchenko shi ma ya ƙi yarda ya yi saranda ga dakarun Rasha, inda a shafin sa na Facebook ya ce ba zai yi ba.
Shi kuwa Kwamandan Askarawan Rashawa a Mariupol, Kanar Mikhail Mizintsev ya faɗa a ranar Lahadi cewa Rasha za ta bari a fice birnin ta hanyoyi biyu kaɗai. Ko da a fice ta Gabacin birnin a shiga Rasha, sai kuma a fice ta yammacin birnin a shiga wasu sassan cikin Ukraniya.
“Duk sojojin da su ka amince suka ajiye makamai, za a bari su fice lami lafiya daga birnin Mariupol.” Inji shi.
Ya kuma bai wa mahukuntan birnin nan da ƙarfe 5 na asubahin ranar Litinin, wato ƙarfe 2 agogon GMT cewa Ukraniya ta bayar da amsa.