Tawagar ‘Yan Majalisar Tarayya daga Najeriya da su ka isa Romaniya domin sa-ido wajen ganin an kwaso sauran ‘yan Najeriya da ke can, su na shan suka daga mutane daban-daban.
Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya Kan Harkokin Ƙasashen Waje, Nkem Anyata-Lafia ne ya bayyana haka.
Yusuf Buba shi ne Shugaban Kwamiti, kuma tawagar ta tafi ne ƙarƙashin Ado Doguwa, Ɗan Majalisa daga Kano.
Sai dai kuma wani jami’in diflomasiyya ya caccaki zaramboton da ‘yan Majalisa ɗin su ka yi, ya na cewa ai ba aikin su ba ne, almubazzaranci ne kawai su ke yi da dukiyar ‘yan Najeriya.
Majalisa dai ta ɗora masu nauyin nauyin zuwa yankin wanda ake yaƙi, domin kwaso dubban ‘yan Najeriya da su ka gudu daga Ukraniya suka tsallaka wasu ƙasashe, domin a kwaso su zuwa Najeriya.
“Ba mu san ranar dawowar mu ba tukunna, amma dai mu na can har sai ranar da aka kammala kwaso ‘yan Najeriya masu son dawowa gida.” Haka Buba ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho.
Majalisa ta yi ƙorafin cewa Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje na jan-ƙafa wajen ƙoƙarin dawo da ‘yan Najeriya ɗin, waɗanda yawancin su ɗalibai ne gida. Dalili kenan su ka shiga lamarin domin a yi gaggawar kwaso su, ganin yadda yaƙin ke ƙara ƙazancewa da muni.
Sai dai kuma ana ganin wannan ba aikin su ba ne, aikin Mai’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje ne, sai kuma hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, ciki har da ofisoshin jakadun ƙasashen waje na Najeriya.
Jide Osuntokun, tsohon Jakadan Najeriya a Jamus, ya ce “tafiyar tawagar ‘yan majalisar Najeriya zuwa Romaniya tsantsar rashin mutunci ne kawai, saboda babu ruwan su, kuma ba aikin su ba ne.
“Rashin mutunci ne kawai da rashin kunyar sanin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Me za su je su yi a can? Shin su jami’an kula da walwalar jama’a ne? Su bar waɗanda ya dace su je su yi aikin su mana.”
Ya ce kawai zarin neman karɓar kuɗaɗen guzuri ne ya kai su. “‘Yan majalisar wace ƙasa aka gani a can idan ba na Najeriya kaɗai ba.”
Wannan jarida ta buga labarin cewa Shugaba Buhari ya ware dala miliyan 8.5 domin kwaso ‘yan Najeriya 5,000 daga Ukraniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kwashi dala miliyan 8.5 domin a kashe su wajen jigilar ‘yan Najeriya aƙalla 5,000 da ke Ukraniya.
Waɗanda za a kwaso ɗin dai su na maƙale ne a can sun rasa hanyar dawowa, tun bayan da yaƙi ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya a ranar 21 Ga Fabrairu.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya ya ce yawancin ‘yan Najeriya mazauna Ukraniya sun gudu, sun tsallaka cikin ƙasar Poland, Romaniya, Hungary da Slovakia.
Ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Zubairu Dada, tare da Ministar Ayyukan Jinƙai da Agaji, ne su ka bayyana haka a Fadar Shugaban Ƙasa, a ƙarshen taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a ranar Laraba.
Matakimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron na ranar Laraba, a Babban Ɗakin Taron Majalisar Zartaswa da ke Fadar Shugaban Ƙasa.
Karamin Ministan Harkokin Waje Dada ya ce an sa hannun amincewa a fidda kuɗaɗen ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji su ka rubuta wasiƙar bai-ɗaya tare ta abin da za’a kashe wajen dawo da ‘yan Najeriya ɗin zuwa gida Najeriya.
Ya ce Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Air Peace ne aka tuntuɓa domin ya samar da jirage uku waɗanda za su riƙa jigila ba dare ba rana, kuma ba ƙaƙƙautawa har sai an kwaso su da gaggawa.
Minista ya ce adadin waɗanda za’a kwaso ɗin akwai 940 a Romaniya, 150 daga Slovakia, 350 daga Poland, waɗanda su ka rigaya su ka yi rajistar son dawowa Najeriya.
Ya ce Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai da Agaji ce ta rubuta takardar buƙatar waɗannan kuɗaɗen domin a yi aikin kwaso yan Najeriya ɗin.
“Kuɗin da aka nema dala miliyan 8.5 kuma nan take Shugaba Muhammadu Buhari ya amince.
“Kuma ya kamata a fahimci cewa ba a biyan kuɗin tikitin jirgi kawai za a kashe kuɗaɗen ba. Kuma ai za a yi ɗaukar nauyin kula da waɗanda su ka zaɓi tsayawa can ƙasashen, kafin ƙura ta lafa su koma.”
Discussion about this post