Amurka ta bayyana saye da hada-hadar fetur da gas ƙasar Rasha. Shugaban Amurka Joe Biden ne ya bayyana wannan takunkumin cinikiyya da Rasha a ranar Talata.
Biden ya ce “maƙasudin katse sayen fetur da gas ɗin Rasha shi ne don a gurgunta wa Rasha tattalin arzikin ta, kuma a matsa wa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya dakatar da yaƙin da ya ke yi da Ukraniya.”
“Mun hana shigo da duk wani fetur da gas da nau’in makamashi daga Rasha. Hakan na nufin Amurka ta daina sayo fetur da gas da makamashi daga Rasha. Mun yi haka ne don mu gyara wa Rasha zama.” Inji Biden.
“Mun ɗauki wannan matsayi ne bayan tuntuɓar ƙasashen da mu ke ɗasawa da su da ƙawayen mu musamman ƙasashen Turai da NATO da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), domin mu tabbatar da mun haɗa kan mu saboda kama-karyar da Rasha ke yi a Ukraniya.”
Sai dai kuma Biden ya ce duk da sun ɗauki matakin ne don a gurgunta Putin da gwamnatin sa, ya na sanar da cewa takunkumin hana cinikayya da Rasha ɗin zai haifar da ƙuncin rayuwa a cikin Amurka.”
“Lokacin da mu ke bayanin bayyana wannan takunkumin, sai da muka yi la’akari da cewa zai haifar mana da ƙuncin rayuwa a Amurika, to amma mafi muhimmanci shi ne ‘yancin ‘yan ƙasar Ukraniya.” Cewar Biden.
A na sa bayanin, shugaban Ukraniya Volodymyr Zelenskyy ya gode wa Amirka bisa ga abin da ya kira riƙe masa maƙogaron Rasha da ta yi.
Aljazeera ta ruwaito cewa ba da fetur ɗin Rasha ne Amurka ta dogara ba. Domin bincike ya nuna cewa kashi 3 bisa 200 na ɗanyen man da Amirka ke saye ne kaɗai daga Rasha, kwatankwacin ganga 209,000 a kowace rana.
Amma ƙasashen Turai ne suka fi dogaro da gas kusan kashi 35 wanda EU ke amfani da shi daga Rasha ake shiga da su ƙasashen Turai ɗin.
Biden ya ce ya san ƙasashen Turai da dama ba za su iya bin sahun sa su daina sayen ɗanyen mai ko gas daga Rasha ba. “Amma Rasha ta yi haka saboda ita ke tace fetur ɗin ta mai yawan fiye da na ƙasashen Turai baki ɗayan su idan aka game wuri ɗaya.