Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin su ta APC ta yi ayyukan da a tahirin Najeriya ba a taɓa yin gwamnatin da ta inganta rayuwa da harkar noma kamar gwamnatin APC ba.
Kakakin Yaɗa Labaran Osinbajo Laolu Akande ne ya fitar da wannan furucin na Osinbajo, a cikin wata takarda da ya aika wa manema labarai a ranar Lahadi.
Akande ya ce wannan furuci a ranar Asabar, a dandalin Eagle Square wurin gangamin APC na Ƙasa, a Abuja.
Ya ce ƙoƙarin da Buhari ya yi na inganta tattalin arziki, daƙile barazanar tsaro, sai kuma yaƙi da rashawa da cin hanci, gagarimin aiki ne wurjanjan.
Osinbajo ya ce riƙo da igiyar samar da ayyukan yi da ƙoƙarin samar da hanyoyin cimma kiwon lafiya, gina ƙasa nagartacciya da sauran nasarori da dama.
“Tilas a yanzu mu fi bayar da hankalin mu wajen ganin ƙudirin mu na fitar da mutum miliyan 100 cikin talauci ya tabbata.
“Ba za mu nuna gajiyawa ba ballantana mu tsaya mu huta. Ba kuma za mu tsaya mu huta ba, Da iznin Ubangiji nan ba da daɗewa ba sai wannan gwamnatin ta mu ta kai ƙasar nan tudun-mun-tsira.”
Ya ce gwamnatin Buhari ta gaji matsaloli, musamman kuma ta ci karo da lokacin korona, amma ta shanye dafin kibau, ta fita daga cikin matsin tattalin arziki.
Ya roƙi ‘yan jam’iyya a ƙara haɗa kai domin a ci gaba da samun nasara.
Mataimakin Shugaba Buhari ɗin ya ce gwamnatin su ta maida hankali wajen samar wa matasa abu uku, na farko ayyuka. Na biyu ayyuka. Na uku ayyuka.