Aƙalla ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 200 jami’an tsaro suka bindige a cikin kwana uku a jihar Neja.
Wannan bayani ya fito daga bakin Kwamishinan Kasa, Raya Karkara, Kula da Masarautu da Harkokin Tsaro, Emmanual Umar.
Umar ya yi wannan bayani a ranar Laraba, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna mai suna Mary Noel-Berje ta bayyana a cikin sanarwar manema labarai, cewa Umar ya yi bayanin a Gidan Gwamnatin Jihar Neja.
Ta ce ya yi bayanin ne bisa umarnin Gwamna Abubakar Bello.
Umar ya ce an bindige kwamandojin ‘yan ta’adda da daman gaske.ya ce daga cikin waɗanda aka karkashe akwai ‘yan bindigar da ke ƙarƙashin sansanin Ali Kawajo, Yello Janbros, Kachalla Halilu da na Bello Turji.
Kwamishinan ya ƙara da cewa an samu wannan gagarimar nasara ce ta dalilin haɗin kan da aka samu na ɓangarorin jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da kuma mutanen yankunan da aka addaba da hare-hare.
Ya ce an kama babura sama da 60 a hannun su, an kama shanun sata masu yawa a hannun su, kuma an ƙwace bindigogi da albarusai. Ya ce makaman da aka kama a hannun su duk an damƙa su a hannun jami’an tsaro.
Sai dai kuma ya ce an rasa rayukan jami’an tsaro biyu, wasu da dama sun ji rauni, amma su na asibiti ana duba lafiyar su.
“A madadin Gwamna Abubakar Sani Bello, ina miƙa ta’aziyyar rashin jami’an tsaron da muka yi ga iyalan su.
Ya ce wannan sadaukarwa da su ka yi, ba abin mantawa ba ce, kuma gwamnati za ta daba haƙƙoƙin su kuma ta yi masu kyakkyawar sakayya.
A ƙarshe ya yaba wa jami’an tsaro, kuma ya roƙi jama’a su riƙa fallasa ɓatagari.
Discussion about this post