Shugaban madu rinjaye na majalisar Tarayya Honarabul Ado Doguwa ya kalubalanci hwamnatin tarayya ta kyale ƴan Najeriya su Mallaki bindigogi fomin kare kansu.
Da ya ke tofa albarkacin bakin sa a mahawarar da aka yi a zauren Majalisar tarayya, Doguwa ya ce lalacewar ta yi yawa yanzu kuma abin ya fi ƙarfin gwamnati yanzu.
” Kawai a kyale mutane su mallaki makamai kawai su kare kansu domin gwamnati ta gaza, jami’an tsaro sun gaza. Babu yadda za a yi, a buɗa kawai duk wanda ya far maka ka kare kanka.
Duk da cewa shine shugaban nasu rinjaye na majalisar kuma Doguwa bai gaza ba wajen faɗin gaskiyar halin da matsalar tsaro ta ke ciki a kasar nan.
” Idan jami’an tsaro sun gaza, bai kamata dukka ƴan kasa su afka cikin wannan bala’i ba, a kyale kowa ya mallaki makami. A haɗa kungiyoyi a rika tunkarar duk wanda ya doso mutane da bala’i.
Idan ba a manta ba a cikin farkon wannan mako ne ƴan bindiga suka tada bam a layin dogo na jirgin kasa daga Abuja-Kaduna.
An kashe mutum 8 sannan da dama an yi garkuwa da su har yanzu suna tsare a hannun ƴan bindigan.
Jihar Kaduna na cikin halin tsaka mai wuya ganin yadda hare-haren ƴan bindiga ya tsananta a ƴan kwanakin nan.