A ranar Litinin Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ya yi wa lauyan EFCC kaca-kaca, tare da yin barazanar cewa zai kori ƙarar da hukumar ta maka Sanata Rochas Okorocha, tsohon Gwamnan Jihar Imo.
Dalilin ragargazar lauyan EFCC kuwa, lamarin ya faru ne saboda lauyan mai suna Cosmos Ugwu ya shaida wa kotu a karo na biyu cewa har yau ya kasa samun Rochas Okorocha ballantana ya damƙa masa sammacin ƙarar sa da EFCC ɗin ta yi.
Wannan ne karo na biyu da lauyan EFCC ya bada uzirin cewa bai samu ganin Okorocha ba, ballantana ya kai masa takardar sammacin sanar da shi an maka shi kotu.
Tun da farko dai EFCC ta kama Okorocha cikin Afrilu, 2021. Sai dai kuma ta bada belin sa daga baya.
EFCC ta sake gurfanar da Okorocha a ranar da ya ƙaddamar da takarar sa ta neman fitowa ya nemi shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC a cikin 2022.
Yayin da aka je kotu a ranar 22 Ga Fabrairu, Mai Shari’a ya nemi Okorocha ya fito domin a fara gabatar masa da tuhumar da ake yi masa, amma babu shi babu alamar sa a kotun.
Mai Shari’a ya ɗage zaman zuwa ranar 28 Ga Maris, 2022 domin lauyan EFCC ya samu damar kai wa Okorocha sammacin sanar da shi an maka shi kotu, kuma ana buƙatar ganin sa a kotun.
Yayin da aka zauna zaman fara sauraren ƙarar, Mai Shari’a ran sa ya ɓaci matuƙa, jin cewa lauya Ugwu bai samu damar sanar da Okorocha batun maka shi kotu da EFCC ɗin ta yi ba.
“Ran Mai Shari’a ya daɗe, ina so a ƙara min wani lokaci domin na samu na aika wa Rochas Okorocha sammaci. Saboda har yau ban samu ganin sa na damƙa masa ba.” Inji Ugwu, lauyan EFCC.
Sai dai kuma wannan furuci ya ɓata wa Mai Shari’a rai matuƙa, har ya yi barazanar korar ƙarar kwata-kwata.
“Bari na fito ƙuru-ƙuru na shaida maka cewa sau biyu kenan ka na bayar da wani dalili na sakaci kawai ba wani abu ba. A matsayin ka na lauya ya zama wajibi ka ɗauki aikin ka da daraja. A yau zan ba ka wa’adi na ƙarshe. Idan ranar da za a dawo kotu ban ga Rochas ba, to zan ƙarar. Saboda ba ka ɗauki shari’ar da muhimmanci ba.”
Daga nan Mai Shari’a ya ce a koma kotu ranar 30 Ga Mayu, 2022, kuma EFCC ta tabbatar Rochas Okorocha ya halarta.