Hukumar Zaɓe Ta Kasa (INEC) ta ce ba za ta bi umarnin kotu ba, inda aka ce ta ayyana sunan wani gwamna, bayan da Babbar Kotun Tarayya ta tsige Gwamna Dave Umahi da Mataimakin sa Kelechi Igwe.
INEC ta bayyana hakan ne a ciki nata sanarwa da Kwamishinan Wayar da Kan Masu Zaɓe, Festus Okoye ya fitar a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce manyan jami’an INEC sun yi taro a ranar Alhamis, sun kuma tattauna batutuwa da dama.
Ya ce daga cikin batutuwan da aka tattauna akwai zaɓen Gwamnan Jihar Osun da kuma canjin sheƙar Gwamna Dave Umahi na Ebonyi, Mataimakin sa Kelechi Igwe da ‘yan Majalisar Jiha 16, waɗanda su ka canja sheƙa daga PDP zuwa APC.
INEC ta ce tilas ta dakatar da miƙa takardar cancanta zama gwamna ga wanda zai maye gurbin Umahi kamar yadda kotu ta yi umarni, saboda an aika wa INEC ɗin wata takardar umarni daban daga wata kotu, wadda ta ci karo da tsige Umahi.
“INEC ta dakatar da batun canja gwamnan Ebonyi da sunan wani ɗan PDP, amma ta bai wa Kwamitin Shawarwarin Shar’u aikin nazarin lamarin, domin ya shawarci hukumar sosai da sosai.
“Daga lokacin da aka tsige Umahi zuwa yau INEC ta karɓi takardun sammaci har guda 12 akan batun.
“Dalili kenan INEC ta dakatar da maye gurbin sunan wani a matsayin halastaccen gwamnan Ebonyi, tunda an ɗaukaka ƙara, kuma mun karɓi sammaci ba ɗaya ba, ba biyu ba mai nuna umarni daga kotu cewa mu dakatar da maye sunan Umahi da na wani.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda kotu ta tsige Gwamnan Ebonyi saboda komawa APC da ya yi, bayan ya ci zaɓe ƙarƙashin PDP
ASHAFA MURNAI
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta tsige Gwamnan David Umahi na Jihar Ebonyi shi da mataimakin sa, saboda komawa APC bayan sun ci zaɓe a ƙarƙashin PDP.
A ranar Talata ce Mai Shari’a Inyang Ekwo ya umarci Gwamna David Umahi da Mataimakin Gwamna Kelechi Igwe su gaggauta ficewa daga Gidan Gwamnanti, domin PDP ta maye gurbin su.
Mai Shari’a ya kuma umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gaggauta karɓar sunayen waɗanda PDP za ta bayar domin su maye gurbin Umahi da mataimakin sa.
An zaɓi Umahi a ƙarƙashin PDP a 2015 da 2019. Amma daga baya ya koma APC ba tare da rikicin komai ba.
Jam’iyyar PDP ta kai ƙarar su, bisa roƙo cewa sun tafi da haƙƙin jam’iyyar PDP, wadda ta ɗauki nauyi da kuma zaɓen su.
Mai Shari’a ya ce Umahi da Mataimakin sa na iya komawa APC, amma ba ɗauke da haƙƙin PDP ba.
“Kuri’a a zaɓen Najeriya ta jam’iyya ce, ba ta ɗan takara ba ce.” Inji Mai Shari’a Ekwo.
Discussion about this post