Ɗan neman takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC Bola Tinubu, ya ragargaji sauran masu neman takara a jam’iyyar, inda ya ce duk ba su cancanta ba, shi kaɗai ne ya cancanta.
Ya yi wannan kakkausan furuci a zauren Majalisar Tarayya, inda ya gana da ‘yan Majalisar Tarayya masu wakiltar APC, bayan ya gana da na Majalisar Dattawa a ranar Laraba.
“Babu wani ɗan takarar da ya kai ni cancanta a cikin waɗanda su ka fito su ka nuna kan su ko waɗanda su ka noƙe ba su kai ga fitowa sun nuna kan su ɗin ba.
“Ni kaɗai ne na fi su gwagwarmaya da faɗi-tashin siyasa na yi sanata, na yi gwamna kuma na san ƙabli da ba’adin yadda zan gyara al’amurra.
“Ni na fi cancanta. Sauran kuwa daga ‘yan a-ci-bulus sai ‘yan miya-ta-yi-zaƙi an zo a ci dabge, sai ‘yan giwa-ta-faɗi sun ɗauko wuƙa su sharɓi tsokar nama. Sai kuma ‘yan arha gasassa.”
Tinubu ya ce ya na alfahari da irin mutane nagari da ya dasa a siyasa waɗanda har yanzu kuma su ke kan bayar da gagarimar gudunmawa.
Ya ce ya je Majalisar Tarayya ne don ya nemi goyon bayan su a tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
‘Tun Tashi Na Nake Da Burin Zama Shugaban Ƙasa’ -Tinubu:
“Ni fa dama tun tashi na na ke da da burin zama shugaban ƙasa, kuma na shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari haka. Na sanar da shi cewa ‘ina son saka ƙafa ta cikin takalmin da za ka cire ta ka ƙafar. Amma ba a kan ƙafar ka kan ɗora tawa ƙafar ba.”
Bunubu ya ce Buhari ya ce masa ya fito don a ga irin gagarimar rawar da zai ƙara takawa wajen inganta dimokraɗiyya.
Tinubu ya ci gaba da bugun ƙirjin cewa har dirigi gare shi a kan fannin ƙididdigar kuɗaɗe.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin ganawar Tinubu da Sanatocin APC, inda ya nemi su taimaka masa ya cika burin shugabancin Najeriya.
Jagoran APC kuma wanda ke sahun gaba wajen ganin APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Bola Tinubu, ya gana da Sanatocin APC, inda ya nemi goyon bayan su domin ya samu nasarar tsayawa takara, kuma ya lashe zaɓen 2023.
Tinubu ya isa Majalisar Dattawa wajen ƙarfe 3 na yamma a ranar Laraba, inda ya gana da Sanatocin APC, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da sauran masu riƙe da muƙamai na APC na Majalisar Dattawa.
Tinubu ya kai masu ziyarar mai kama da kamfen, makonni biyu kafin taron gangamin APC, wanda za a zaɓi shugabannin jam’iyya.
Tun cikin watan Janairu ne TInubu ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari aniyar sa ta neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Tinubu ya shaida wa dattawan Sanatocin APC cewa ga fa zaɓe ya gabato, amma fa ba shi iya yin kamfen shi kaɗai.
Ya ce dalili kenan ya ke nema da buƙatar goyon bayan su domin su taimaka ya cika burin sa na zama shugaban ƙasa.
Ya roƙi su taimaka ya ci zaɓen fidda-gwanin APC domin ya gaji Shugaba Buhari.
Ya ce ganin yadda ya yi gwamna tsawon shekaru takwas a Legas da kuma kasancewa ya taɓa yin kamata, to ya cancanci zama shugaban ƙasa.
Discussion about this post