Bayan matsi da suka sha daga wasu gwamnonin kasar nan ƴan takarar shugabancin APC 6 sun amince su mara wa zaɓin shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shugabannin jam’iyyar da za a yi a yau Asabar.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Legas, Sanwo-Olu da na Ekiti Kayode Fayemi ne suka yi ta faɗi tashi suna kai komo don ganin ƴan takaran da suka ki amincewa sun janye kowa ya ɗau seti, an yi abinda ya dace kada a watsa wa Buhari kasa a ido a wurin taro.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ƴan takara suka lashi takobin lallai sai dai a yi zaɓe amma ba za su amince da zaɓin Buhari ba.
Majiyoyi da dama da suka tattauna da PREMIUM TIMES sun tabbatar mana cewa lallai akwai fa sauran rina a kaba domin ƴan takaran shugaban jam’iyyar ba su amince da zaɓin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
” Bari in gaya maka ka sani babu ɗaya daga cikin ƴan takaran da ya amince da zabin Abdullahi Adamu wato zaɓin Buhari ya zama shugaban jam’iyyar APC. Saboda haka ina tabbatar maka cewa yanzu haka yan takaran sun ce kowa tasa ta fishheshi kawai. Iya ruwa fidda kai.
Sai dai kuma wani abu da PREMIUM TIMES ta jiyo shine ƴan takaran basu ji daɗin yadda shugaba Buhari ya yi musu a lokacin da ya gana da su bane.
Majiya ta shaida mana cewa bayan duka ƴan takararn sun hallara a fadar shugaba Buhar, sai ya karanta jawabinsa inda a karshe ya bayyana cewa yana goyon bayan sanata Adamu Abdullahi ya zama shugaban jam’iyyar. Daga sai ya kama gaban sa yayi tafiyar sa ya barsu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
” Wannan abu ya bata wa ƴan takaran rai. Wasu sun ce shugaba Buhari bai ɗauke su a bakin komai ba saboda haka sai sun ga abinda ya ture wa buzu naɗi a wajen wannan taro.
Wasu deliget din da suka halarci wurin taron sun shaida wa wakilin mu cewa har yanzu ba su ba a sanar musu da wanda za su zaɓa ba. Amma da yawa kuma sun ce sun samu sakon lallai a mara wa Adamu Abdullahi baya ya zama shugaban jam’iyyar.
Wurin taro dai ya cika ya batse. Ana ta hada-hada da shirin zaɓe, haka kuma otel otel a Abuja gana ɗaya sun cika babu masaka tsinke.