Ɗan takarar gwamna na ƙarƙashin PDP a Jihar Gombe, Mohammed Jibrin ya zargi Gwamnatin Jihar Gombe da ruguza masa ofishin kamfen a babban birnin jihar.
Jibrin ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa an rushe masa ofishin kamfen cikin gadara da kuma nuna ƙin bin umarnin kotu da gwamnatin jihar ta yi.
Ya ce kotu ta bayar da umarnin cewa kada a rusa masa ofishin, wanda ke ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Gombe Good Leadership Association.
Amma kuma gwamnatin jihar Gombe ta ƙaryata zargin daya yi mata, ta ce an rushe ginin ne saboda masu ginin ba su cika sharuɗɗan da hukumar kula da gine-gine ta shimfiɗa ba, a lokacin da su ke yin ginin.
“An ruguza mana ofishin kamfen, wanda kuma Gwamnatin Jihar Gombe ce ta rusa shi. Abin ya ba mu mamaki.” Haka ɗan takarar ya shaida wa manema labarai.
“Cikin watan Disamba 2021, mun shirya kammala wannan ofishin kamfen, sai mu ka je ofishin hukumar kula da gine-gine, muka sabunta tsarin ginin da muke da shi a da na farko, wanda aka amince mana shi tun cikin 2018.
“Ruguza mana ofishi kawai bi-ta-da-ƙullin siyasa ne gwamna ya ke yi mana. Saboda mun sanar da hukumar kula da gine-gine komai kuma ta amince. Kuma wannan rusa gini fatali ne da umarnin Babbar Kotun Jihar Gombe, wacce ta ce kada gwamnati ko magoya bayan ta ko ajen-ajen ɗin ta ko ma wani na ta ya ruguza mana gini.” Inji shi.
Martanin Gwamnatin Gombe:
Hukumar Kula da Tsara Gine-gine A Birni (GISUPDA), ta ƙaryata zargin da ɗan takarar ya yi, da ya ce an yi ƙarfa-ƙarfa da take umarnin kotu aka rusa masa ofishin kamfen.
Cikin wata sanarwa da Shugaban GISUPDA Bitrus Bilal ya fitar a ranar Laraba, hukumar a cewar sa ta rusa ginin saboda an ƙi bin tsarin da Dokar Jihar Gombe ta GOSUPDA ta shimfiɗa.
“A ranar 29 Ga Disamba, ‘Gombe Good Leadership Association’ ta nemi iznin kafa allon sanbodi na wucin-gadi, kuma aka ba ta iznin bayan ta cika sharuɗɗa.
“Sharuɗɗan sun haɗa da kawo wa wannan hukuma taswirar tsarin gini da takardun haƙƙin mallaka da kuma rubutacciyar wasiƙar amincewa da abin da aka ce shi za a yi a ofishin.”
GOSUPDA ta ce amma Gombe Good Leadership Association duk ba ta cika waɗannan sharuɗɗa da aka gindiya ba.
“Ba su cika sharuɗɗa ba sai kuma su ka ci gaba da gina abin da ba shi su ka rubuto mana cewa za su yi ba. Wato gini na dindindin su ka yi a wurin.
“Wannan hukuma ta aika masu da takardar su dakatar da gini har sau biyu, a ranakun 9 Ga Fabrairu da 2 Ga Maris, 2022.
“Mun yi masu rubutun dakatar da gini, amma su ka karya doka, su ka ci gaba da aiki, har su ka shafa filasta a kan rubutun da dakatar da ginin da muka yi masu. Wannan kuwa ya saɓa wa dokar GOSUPDA ta sashe na 27, ta shekarar 2011.”
“Sannan kuma GOSUPDA ta lura da cewa tunda ofishin ‘yan adawa ne, wurin ya yi kusa da Masaukin Shugaban Ƙasa. Hakan zai iya kawo barazana ga tsaro. Saboda haka muka rusa ginin.”
GOSUPDA ta ce aikin ta ne na hukuma ta yi, ba umarnin wata jam’iyya ko wani mutum ta bi ba.
Discussion about this post