Tsohon Gwamnan Jihar Barno Ali Modu Sheriff ya bayyana matsayin sa a kan wanda zai shugabanci APC ta ƙasa, a gangamin ranar 26 Ga Maris.
Sheriff ya ce shi dai a shirye ya ke ya bi kuma ya amince tare da zaɓen duk ɗan takarar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna da ya ce shi za a zaɓa.
Wannan furuci na Sheriff ya fito ne mako ɗaya bayan da APC ta fitar da jadawalin yanayin zaɓen shugabannin da za ta yi a ranar 26 Ga Maris. Haka kuma APC ta fitar da shiyyoyin da kowane ɗan takarar muƙaman shugabannin APC za su fito.
Jam’iyyar APC dai ta miƙa takarar shugaban jam’iyya zuwa cikin yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da aka fi sani da Middle Belt.
Sai dai kuma akwai wasu gaggan jam’iyyar APC masu kai gwauro da marin ganin an yi sauye-sauyen inda shugabannin jam’iyya za su fito.
PREMIUM TIMES Hausa ba ta da masaniyar ko har da Sanata Modu Sheriff cikin masu haƙilon ganin an yi sauye-sauyen.
Amma kuma Sheriff ya ce batun raba muƙaman shugabannin APC da aka fitar shiyya-shiyya, duk ji-ta-ji-ta ce kawai. “Ni duk wanda Buhari ya nuna ya ce a zaɓa, to shi zan bi.”
Ya ce har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari da uwar jam’iyya ba su ce ga wanda za a zaɓa ba.
“Ina cikin ‘yan takara, saboda na cancanta, amma duk wanda Buhari ya nuna, shi zan bi.” Inji Sheriff.
Yadda APC Ta Raba Muƙaman Shugabannin Ta Da Shiyyoyin Da Za Su Fito:
ASHAFA MURNAI
Shiyyar Kudu Maso Kudu: Akwa Ibom, Bayelsa, Cross Riba, Delta, Edo da Ribas:
Daga waɗannan jihohi ne za a zaɓi:
1. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu maso Kudu.
2. Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai.
3. Shugabar Mata ta Ƙasa.
4. Mataimakin Ma’ajin Kuɗaɗen Jam’iyya.
5. Mataimakin Sakataren Walwala na Ƙasa
Shiyyar Kudu Maso Yamma: Ekiti, Legas, Ogun, Ondo, Osun, Oyo:
1. Sakataren APC na Ƙasa.
2. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu maso Yamma.
3. Shugaban Matasan APC na Ƙasa.
4. Mataimakin Mai Binciken Kuɗaɗen Jam’iyya.
Shiyyar Kudu Maso Gabas: Abiya, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo:
1. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu Baki Ɗaya.
2. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu maso Gabas.
3. Ma’ajin APC na Ƙasa.
4. Sakataren Walwala na Ƙasa.
5. Mataimakin Sakataren Shirye-shiryen APC na Ƙasa.
Shiyyar Arewa Maso Gabas: Adamawa, Bauchi, Barno, Gombe, Taraba, Yobe:
1. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Arewa Baki Ɗaya
2. Mai Binciken Kuɗaɗe na Ƙasa.
3. Mataimakin Sakataren Kuɗaɗe.
4. Mataimakiyar Shugabar Matan Jam’iyya.
Shiyyar Arewa Ta Tsakiya: Benuwai, Kogi, Kwara, Neja, Fatakwal:
1. Shugaban Jam’iyya na Ƙasa.
2. Mataimakin Sakataren Jam’iyya.
3. Mataimakin Lauyan Jam’iyya.
4. Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai.
Shiyyar Arewa Maso Yamma: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, Zamfara:
1. Lauyan Jam’iyya Mai Bada Shawara A Fannin Shari’a.
2. Sakataren Shirye-shirye Na Ƙasa.
3. Sakataren Kuɗaɗen Jam’iyya.
4. Mataimakin Shugaban Matasan APC.
A Kula: Kowace shiyya za a zaɓi Mataimakin Shugaba, Sakataren Shiyya, Shugaban Matasan Shiyya, Sakataren Shirye-shirye Na Shiyya, Shugabar Mata Ta Shiyya da kuma Shugaban Ƙungiyar Naƙasassun Jam’iyya na Shiyya.