A wannan mako zamu fara sharhin namu ne da danbarwar dake faruwa a jam’iyar APC, ga dukkanin masu bibiyar al’amuran siyasa na sane da yadda rikice-rikice ke damun jam’iyar, kama daga rikicin shugabanci a mataki na tarayya har zuwa ricin jahohi wadda yaki ci yaki cinyewa har kawo yanzu da jam’iyar ke dabda gabatar da babban taronta na kasa domin zaben shuwabannin dasu jagoranci ragamar jam’iyar zuwa kakar zabe mai zuwa. In mai karatu zai iya tunawa, a baya rikicin daya dabibye jam’iyar ne yayi sanadiyar korar shugaban jam’iyar na farko wato John Odigie Oyegun bayan tsundima jam’iyar da yayi acikin rikice-rikice musamman na cikin gida wadda ya haifarwa da jam’iyar rasa wasu jahohi masu tarin yawa. Wannan ne yasa ganin yadda jam’iyar take neman wargatsewa yasa shugaban kasa ya bada umarnin tsige shugaban inda a shekarar 2018 aka maye gurbinsa da tsohon Gwabnan jahar Edo, wato Comrade Adams Oshiomhole.
Zuwan Comrade Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyar ya bawa al’umma da dama musamman mabiya jam’iyr Karfin gwiwar ganin jam’iyar zata iya dawowa seti. Sai dai kash, ba a dade da zuwan nasa ba sai rikice-rikice musamman wurin fitar da yan takarkari ya sake kunno kai acikin jam’iyar. Kadan daga cikin manyan asarar da tsohon shugaban jam’iyar wato Oshiomhole yayiwa jam’iar sun hada da rasa kujerar gwabnan jahar Edo bayan yayi rigima da Gwabna mai ci, wato Godwin Obaseki a jahar, wadda daga karshe ya fice daga jam’iyar ta APC ya koma jam’iyar PDP kuma ya ka da dan takarar da shi Oshiomhole ya tsayar. Sai kuma wani rikici da ya sake kuluwa a jahar Imo tsakanin Gwabna mai ci a waccan loakcin wato Rochas Okorocha da Gwabna mai ci a yanzu wato Hope Uzodinme, wutar da har yanzu tana ci takanin mutanan guda biyu. Sai dai duk wadannan basu sa jagororin jam’iyar sun hankalta ba kuma sun dau matakin da ya dace akan tsohon shugaban jam’iyar har sa da yayiwa jam’iyar asarar dukkanin kujerun da ta ci a kakar zabe ta shekarar 2019 jahar Zamfara bayan daya hada rikici tsakanin Gwabna Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sannan muhukunta a jam’iyar suka dauki mataki sallamarsa daga shugabancin jam’iyar.
Jim kadan da korar Adams Oshiomhole daga shugabancin ne sai jam’iyar ta kafa shugabancin rikon kwarya karkashin jagorancin Gwabnan Yobe, wato Mai Mala Buni. Tun farkon shugabancin nasa, al’ummar da dama sun ta korafi kan yadda aka bashi jagorancin jam’iyar ganin cewa shi gwabna ne mai ci. Amma dai wannan bai hana shi rikon jam’yar ba har na tsawon kusan sheakaru biyu Kafin daga bisani wasu jiga gigai acikin jam’iyar su jagoranci tsige shi daga shugabancin na rikon kwarya kamar yadda Gwabnan Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’I ya shedawa kafar talabijin ta Channels. Wannan kora da akayiwa Buni ta sake tayar da wata kurar a jam’iyar inda mutane da dama muasamman yan jam’iyar ke tofa albarkacin bakinsu. Ko a ranar asabar din data gabata an jiyo shugaba Muhammadu Buhari na kira da yan jam’iyar da su guji cin zarafin juna, dayin abunda ka iya jefa jam’iyar cikin rudani ko kuma abunda ya sami jam’iyar PDP a shekarar 2015. Nan zamu ajiye wannan batu, zamu ci gaba da bibiyar lamarin dan ganin yadda zata karke game da shugabancin jam’iyar.
Bari mu dawo jahar Kano muyi duba da halin da siyasar Madugun Darikar Kwankwaasiya take ciki. A hakikanin gaskiya siyasar madugun Kawnkwasiya ta fara shiga halin ni ‘ya su, dan kuwa madugun tuni ya raba gari da jam’iyar PDP bayan da yake zargin ba a yi masa adalci a shugabancin jam’iyar.
Wannan ce tasa a kwanankin baya ya kafa wata kungiya dayake tunanin zaiyi anfani da ita domin cimma burinsa na zama shugaban Najeriya. Jim kadan bayan kafa wannan kungiya sai kuma aka jiyo madugun ya hada kayansa ya koma jam’iyar New Nigerian People’s Party (NNPP) tare da wasu mabiyansa. Sai dai abunda ya bawa al’umma mamaki shi ne yadda wasu daga cikin jiga jigan tafiyar kwankwasiyar kamarsu Dakta Yunusa Adamu Dangwani, Nuhu Danburan Abubakar, Yusuf Danbatta, Hadiza Adedo da Injiniya Bashir su ki yin mubaya’a ga shugaban nasu. Wannan dai masana na ganin cewa baya rasa nasaba da kakaben da wadannan mabiya suke tsammanin shugaban nasu yanayi musu musamman ta wurin tsayar da yan takarkaru.
To ko shin mai wannan kaura ta Rabi’u Kwankwaso ke nunawa a game da tafiyarsa tasa? Tabbas zamu iya cewa siyasar madugun ta fara dishashewa, kuma tabbas in dai a wannan karo baiyi wani abun azo a gani ba musamman na kafa gwabnati a jahar Kano inda ake ganin nan ne kawai yake da magoya baya masu yawa, to shakka babu za’a rufe shafinsa a siyasar Najeriya daga kakar zaben 2023.
Bari mu karkare wannan sharhi namu da harkokin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga wadda yaki ci yaki cinyewa a yanki Arewa masu Yamma. A makwon da mukayi bankwana da shi ne aka sami labarin cewa yan bindiga sun kai hari kan motacin Mataikin Gwabnan Kebbi inda suka halaka wasu jami’an tsaro dake kare lafiyar Mataimakin Gwabnan. Hakazalika a jahar ta Kebbi dai an sami labarin yan bindigar sun kashe masu tsaro na sa kai fiye da guda 60 tare da wasu sojoji wadda har ya haifar da zanga-zanga daga matan sojojin da aka kashe.
Wannan batu na tsaro tabbas babban al’amari ne wadda ya kamata mahukunta su tashi tsaye su mai da hankali domin kawo karshen wannan ta’asa da yan bindigar ke aikatawa. Domin kuwa in har ‘yan bindigar zasu iya kaiwa motacin mataikin gwabna hari har su kashe wasu daga cikin masu bashi tsaro to lelle al’umma suna cikin tashin hankali.
Discussion about this post