Babban Lauya kuma tsohon Antoni Janar na Najeriya, Kanu Igabi wanda ke lauyan Abba Kyari, ya shaida wa kotu cewa idan aka yi gaggawar yanke wa dillalan da su ka amsa laifin su hukunci, to hakan na iya shafar shari’ar da ke wa Abba Kyari da sauran ‘yan sanda huɗu da ba su amsa laifin su ba.
Igabi ya yi wannan bayani ne jim kaɗan bayan da lauyan NDLEA Joseph Sunday ya roƙi kotu da ta fara shirin shari’ar biyu ɗin da su ka amsa laifin su domin a yanke masu hukunci nan gaba ba tare da ɓata lokaci ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda dillalan biyu su ka shaida wa kotu cewa sun amsa laifin su na shigo da hodar ibilis cikin Najeriya.
Sai dai kuma Kanu Igabi ya nuna damuwa cewa, ba mamaki waɗanda “suka amsa laifin su ɗin sun amsa ne a cikin rashin sanin shari’a.”
Sai dai kuma lauyan waɗanda su ka amsa laifin su ɗin mai suna Mista Okenyi ya ce ba su amsa laifin su a cikin rashin sanin shari’a ba, domin har sassauci su ka nemi kotu ta yi masu, bayan sun amsa laifin su.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya ɗage shari’ar zuwa ranakun 14 da 28 Ga Maris, domin tattauna batun beli.
Kuma ya nemi ɓangaren lauyan su Kyari da na NDLEA su bijiro wa kotu da ayoyi a cikin kundin tsarin mulki na buƙatar gaggauta hukunta waɗanda su ka amsa laifin su ɗin ko kuma jinkirtawa.
Ranar Litinin ce dillalan hodar sun amsa laifin su, Kyari da sauran ‘yan sanda ba su amsa laifi ba.
Waɗanda ke cikin zauren shari’ar da aka fara ta su Abba Kyari a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, sun cika da mamaki, yayin da mutum biyu da ake zargin sun shigo da hodar ibilis daga Brazil da Habasha, su ka amsa laifin su, ba tare da wata jayayya ba.
Chibunma Patrick da Emeka Alphonsus Ezenwanne sun amsa laifin tuhuma mai lamba ta 5, 6 da na 7, waɗanda duk ke da nasaba da laifin shigo da muggan ƙwayoyi.
“Ran Mai Shari’a Ya Daɗe, na aikata laifin.” Haka kowanen su ya sanar wa kotu a ba’asin su da aka shigar daban-daban.
An karanta masu cewa sun karya dokar Hukumar NDLEA, ta Sashe na 14(b), ta 30 a ƙarƙashin Dokar 2004.
An tuhume-tuhume su da shigo da koken a filin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, a ranar 25 Ga Janairu, 2022.
Da Gaggan Dillalan Hodar Ibilis Daga Brazil -NDLEA:
Hukumar Hana Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA), ta nesanta jami’anta daga tu’ammali da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 25 ɗin da aka kama wasu gungun ‘yan sanda da ita, bisa jagorancin dakataccen ɗan sanda Mataimakin Kwamishina Abba Kyari.
Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa.
Ya ƙaryata alaƙar da ake ce ke tsakanin jami’an NDLEA na filin jirgin saman Enugu da waɗanda su ka shigo da hodar ibilis a filin jirgin daga Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.
Babafemi ya ce labarin ƙarya ce kawai wasu ‘yan sanda suka riƙa watsawa.
Babafemi ya ce bincike ya nuna cewa Abba Kyari da gungun wasu ‘yan sanda yaran sa ne ke da alaƙar kai-tsaye da wasu gaggan dillalan muggan ƙwayoyi a Brazil.
“Bincike ya tabbatar cewa Abba Kyari ne da yaran sa dillalan ƙwayoyin su ka yi mu’amala tare. Kuma binciken ya nuna yadda su ke aiki tare.”
Mugu Ba Shi Da Kama: Yadda Abba Kyari Da Yaran Sa Ke Shirya Safarar Muggan Ƙwayoyi Da Gaggan ‘Yan Ƙwayar Brazil:
“Idan za a iya tunawa bayan NDLEA ta nemi Hukumar ‘Yan Sanda ta ba su Abba Kyari da yaran sa domin su yi masu tambayoyi, ‘yan sandan sun yi masu tambayoyi sannan suka damƙa su ga NDLEA, tare da rahoton tambayoyin da suka yi masu.” Haka Babafemi ya bayyana.
Babafemi ya ce wani ɗan sanda da ke cikin gungun yaran Abba Kyari mai suna James Bawa, ya tabbatar cewa ya yi magana da wani ejan ɗin dillalin ‘yan ƙwaya da ke Brazil, kafin a shigo da sunƙin ƙwayoyi a ranar 19 Ga Janairu, 2022.