Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta tsige Gwamnan David Umahi na Jihar Ebonyi shi da mataimakin sa, saboda komawa APC bayan sun ci zaɓe a ƙarƙashin PDP.
A ranar Talata ce Mai Shari’a Inyang Ekwo ya umarci Gwamna Divid Umahi da Mataimakin Gwamna Kelechi Igwe su gaggauta ficewa daga Gidan Gwamnanti, domin PDP ta maye gurbin su.
Mai Shari’a ya kuma umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gaggauta karɓar sunayen waɗanda PDP za ta bayar domin su maye gurbin Umahi da mataimakin sa.
An zaɓi Umahi a ƙarƙashin PDP a 2015 da 2019. Amma daga baya ya koma APC ba tare da rikicin komai ba.
Jam’iyyar PDP ta kai ƙarar su, bisa roƙo cewa sun tafi da haƙƙin jam’iyyar PDP, wadda ta ɗauki nauyi da kuma zaɓen su.
Mai Shari’a ya ce Umahi da Mataimakin sa na iya komawa APC, amma ba ɗauke da haƙƙin PDP ba.
“Kuri’a a zaɓen Najeriya ta jam’iyya ce, ba ta ɗan takara ba ce.” Inji Mai Shari’a Ekwo.