Mazauna kauyen Guga a jihar Katsina sun musanta ceto mutum 36 din da sojoji suka ce sun yi cewa sai da suka biya sama da Naira miliyan 20 kudin fansa kafin aka saki ƴan uwansu.
Jama’an kauyen sun ce sai da suka biya sama da naira miliyan 20 kafin aka sako musu ƴan uwa.
BBC Hausa ta buga ta ce dakarun ‘ Najeriya sun ceto wadannan mutane ne bayan arangama da suka yi da ƴan bindigan.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa a ranar 7 ga Faburairu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 36 inda a ciki akwai dagacen kauyen Alhaji Umaru a cikin kauyen Guga.
Jaridar ta ce an sako wadannan mutane bayan sun yi wata daya a hannun ‘yan bindiga bayan sun biya kudin fansa har naira miliyan 26.
Surikin dagacen Nafiu Muhammadu ya ce ‘yan bindigan sun kira iyalin dagacen kwanaki biyu bayan sun yi garkuwa da su sannan suka bukaci a biya su naira miliyan 30 kudin fansa.
“Maharan na tattaunawa da kanen dagacen da wasu dattawa a kauyen sannan lokacin da aka fada musu cewa ba za a iya biyan kudin da suka nema ba sai maharan suka ce za su tattauna da shugabansu daga baya za su neme mu.
Yadda muka tara Naira miliyan 26
A wata takarda da aka fitar a madadin mazauna kauyen Mahadi Dan – Binta ya bayyana cewa mutanen kauyen da wasu abokan arziki suka hadu suka tara Naira miliyan 26 din da aka biya ‘yan bindigan.
Dan-Binta ya ce a ranar 25 ga Maris, 2022, BBC Hausa ta buga cewa sojoji sun ceto mutane 36 din da aka yi garkuwa da su daga kauyen.
“Ina so in karyata wannan magana da rundunar sojojin Najeriya ta yi domin ba gaskiya bane.
Dan-Binta wanda matarsa da ‘yarsa na cikin mutum 36 din da aka yi garkuwa da su ya ce mazauna kauyen sun yi biya sau biyu kafin ‘yan bindigan suka sako mutanen.
” Sojoji sun taimaka wajen karbo mutane daga hannun ‘yan bindiga kuma suka damka su a hannun mu.
“Bayan sun karbi Naira miliyan 11 kudin fansa karo na biyu sai ‘yan bindigan suka ce muje mu jira su a Faskari ko ‘Yankara. Kafin nan saida suka nuna mana hutunan waɗanda suka yi garkuwa da muka tabbatar suna nan da ran su.
” Da misalin karfe biyar na yamma aka kira ni aka ce in xo kwashi ƴan uwan mu da aka yi garkuwa da du.
A karshe Dan – Binta, ya yabawa sojojin dake aiki a wannan yanki da kokari da suke yi na kare rayuka da duniyoyin mutane. Sannan kuma ya kara da cewa ya fito yayi wannan bayani ne domin mutane su san irin kokarin da jama’a suka yi wajen karɓo ƴan uwansu a hannun ƴan bindiga.