Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ta kama masu aikata miyagun aiyukka mutum 1,464 sannan ta saurari kararraki 850 a cikin shekaru biyu a jihar.
Kakakin rundunar Mohammed Wakil ya sanar da haka a taron inganta hadin Kai da zaman lafiya da hukumar NIPR ta shirya ranar a garin Bauchi.
Ya ce rundunar ta kama masu garkuwa da mutane, masu yi wa mata fyade, ‘yan fashi da makami, kisa da dai sauran su.
Wakil ya ce rundunar ta saurari kararraki da suka shafi fashi da makami guda 112 sannan ta kai ‘yan fashi da makami mutum 287 kotu.
Rundunar ta saurari kararrakin yin garkuwa da mutane 74 sannan ta kai su kotu.
Jami’an tsaron sun kama kuma sun kai mutum 231 kotu bisa laifin aikata fyade sau 186 a jihar.
“Rundunar ta saurari kararakin da suka shafi kashekashe 110 kuma ta kai mutum 206 dake da alaka da aikata kisan kotu sannan rundunar ta saurari kararrakin sata guda 30.
“Rundunar ta kama kaya da kudi da suka kai naira miliyan 101.
“An Kuma kama bindigogi guda 88, AK-47 guda 25, kananan bindigogi guda uku, harsasai 6,466 da sauran su.