Jam’iyyar APC mai mulki ta afka cikin ruɗani bayan gwamnan Neja Abubakar Bello ya rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar na jihohi a Abuja a matsayinsa na sabon shugaba.
Gwamnan jihar Neja Bello ne ya ke jagorantar jam’iyyar a madadin Mala Buni da shine ke shugabancin jam’iyyar tun bayan da jam’iyar ta yi sallama da Adams Oshiomhole a 2020.
An ruwaito cewa wasu gwamnoni da suka haɗa da na Kaduna, Jigawa, Ekiti, Filato,Neja sun garzaya wurin shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda suka kai masa kukan yadda Mala Buni ke kitsa tuggun rugurguza zaɓen jam’iyyar ta Kasa wanda za a yi a karshen watan Maris.
Wani gwamna daga kudu ya bayyana cewa a gaban sa shugaba Buhari a wajen wannan taro ya bada umarnin a musanya Buni da Bello sabo da matsalolin da ya jefa jam’iyyar a ciki
Da yake tattaunawa da ƴan jarida a ofishin jam’iyyar a Abuja bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi da yayi, gwamna Bello ya ce ya rantsar da su ne a madadin gwamna Buni da bashi kasar yanzu haka.
” Gwamna Buni bashi Najeriya ina aiki ne a madadin sa ba wai an musanya shi da ni bane.
Sai dai kuma bincike mai zurfi da aka yi sun nuna cewa an gano lallai akwai wata makarkashiya da Buni da mutanen sa ke shiryawa na ganin an tarwatsa zaɓen jam’iyyar na kasa da ke tafe.
Jam’iyyar zata gudanar da taron kwamitin zartaswa wanda shugaba Buhari zai halaeta amma ta yanar gizo. A wannan taro ne ake kyautata zaton gwamna Buni zai mika takardar ajiye aiki a matsayin sa na shugaban jam’iyyar maimakon a bayyana tsigeshi kai tsaye.
Idan ba a manta ba, wata kotu a Abuja ta yanke hukuncin a dakatar da taron kasa da jam’iyyar za ta yi a karshen wannan wata.
Discussion about this post