Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa an kashe mutum biyu sannan wasu mutum biyar sun ji rauni a rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Guri.
Kakakin rundunar Lawan Adam ya ce rikicin ya auku ne ranar Juma’a a dajin Magirami.
Sai dai Kuma mazauna karamar hukumar sun ce akwai yiwuwar an kashe mutane da dama a rikicin saboda wasu sun bace tun a ranar Juma’a ba a gan su ba.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani manomi da kibiya bayan sun yi masa barna a gona.
A ranar Juma’a wasu mazaunan Guri sun fantsama kasuwan garin inda suka far wa wasu makiyaya domin rama kisan manomin da aka yi.
Nan da nan rundunar ‘yan sandan Guri tare da hadin gwiwar ‘Operation Puff Adder’ da ‘Operation Sallama’ a karkashin jagorancin Muhammad Usman suka nufi kasuwar Guri domin tabbatar da tsaro.
Jami’an tsaro sun tsinci gawar wani mazaunin Guri Umar Abdulrauf mai shekara 35 da wani mutum da har yanzu ba a san sunan sa ba.
Sannan mutum biyar din da suka ji rauni a jikin su an kai su asibitin Hadeja likitoci na duba su.
Adam ya ce jami’an tsaron sun kama wani mazaunin Galdimari Fulani Adamu Ahmadu mai shekara 25 saboda yana da hannu a tada rikicin
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Tafida da wasu manyan hafisan tsaro sun ziyarci wurin sannan an aika da jami’an tsaron da za su rika sintiri a karamar hukumar domin samar da tsaro.
Adam ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo sauran mutanen da suka tada rikicin.
Ya ce da zaran an kama su za a kai su kotu domin yanke musu hukunci.