Kamfanin jirgin saman AZMAN ya dakatar da tashi da sauka a filin jirgin saman Kaduna daga ranar Talata.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa wanda kamfanin ta fitar ranar Talata a Kaduna.
Idan ba a manta ba a karshen makon jiya ne ƴan bindiga suka kai hari filin jirgin saman inda suka kashe wani mutum ɗaya kafin jami’an tsaro su fatattake su.
Azman ya ce ba zai yiwu ace ana aiki kuma ana samun matsalar tsaro a filin jirgin.
” Za mu ɗan dakata tukunna har sai abubuwa sun ɗan tsagaita kafin nan sai kuma mu bayyana matakin mu na gaba.
Hare-haren ƴan ta’adda ya dawo gadan-gadan a jihar Kaduna inda a kwanakinnan mahara sun rika kai hare-hare a wurare babu kakkautawa.
Sama da mutum 900 ne suka afka wa tarkon mahara a hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.
Haka kuma a cikin makon jiya an kashe sama da mutum 30 a harin Kagoro, baya ga gidaje sama da 200 da aka kona.
A karshen makon jiya an kashe akalla mutum 40 a karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna bayan mahara sun afkawa wasu ƙauyuka a yankin.
Jihohin Kaduna, Neja, Katsina da Zamfara wanda duk sun yi iyaka da juna na fama da matsanancin hare-haren ƴan bindiga babu ƙakkutawa.
Discussion about this post