A daidai sabon gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya yayi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Anambra, kowa kuma ya zauna yana sauraren abin da zai biyo baya na jawabai, sai mai dakin tsohon gwamnan jihar da suka kammala mulki, Ebelechi Obiano ta mike tsaye ta garzaya inda Bianca Ojuchukwu ta ke zaune.
Isar ta ke da wuya sai ta gaura mata mari a fuska. Kan fin kace wani abu jami’an tsaro sun kai mata dauki an janye ta a wannan wuri.
Da yake babu wanda yayi tsammanin hakan zai faru ita kanta Bianca Ojukwu sai da aka janye ta daga wannan wuri aka tafi da ita.
Da yake an riga an rantsar da sabon gwamna, Charles Soludu, tsohon gwamna da matar sa Ebelechi suma sun tattara sun fice daga wurin taron a wannan lokaci.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya da ta buga labarin ta ce, sabon gwamna Soludo ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin cigaban jihar ta Anambra.