” Mataimakin na Osinbajo na nan, idan bana nan shine doka ta ba shi damar riƙe kasa. Saboda haka babu abinda zai canja. Sannan kuma ga sakataren gwamnatin kasa da shufaban ma’aikatan fadar gwamnati.”
Idan ba manta ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida a makon jiya cewa zai zarce kasar Birtaniya ganin likita daga taro a kasar Kenya a cikin makon jiya.
A ranar Talata ce Buhari ya bar Najeriya ya lula Kenya, inda zai halarci taron magance ƙalubalen rashin kyawon yanayi a Afrika. Wannan taro dai shi ne na 50, kuma a ranakun 3 da 4 Ga Maris.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, ya ce Buhari zai shafe makonni biyu a Landan ɗin ana duba lafiyar sa.
Adesina ya ce waɗanda za su yi wa Buhari rakiya sun haɗa da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Geoffrey Onyema, Ƙaramar Ministar Muhalli, Sharon Ikeazor, Mashawarci Kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, Shugaban NIA Ahmed Rufai Abubakar Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke zaune Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa.
Idan ba a manta ba, kafin a zaɓi Buhari a 2015, daga cikin kamfen da alƙawurran da Buhari ya riƙa yi su ne idan aka zaɓe shi, zai gyara asibitoci sannan kuma shi da manyan jami’an gwamnatin sa ba za su riƙa fita ƙasashen waje ganin likita ba.
Sai dai kuma tsawon shekaru bakwai da Buhari ya yi kan mulki, ya ci gaba da fita Ingila yin doguwa da gajerar jiyya da zuwa ganin likita ya dawo duk a Landan.
A nan Najeriya kuwa likitoci sun sha fama da yajin aiki sanadiyyar kasa cika masu alƙawarin da gwamnatin Buhari ta ɗaukar masu na biyan su haƙƙoƙin su.