Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana cewa zai tausa jigon APC Bola Tinubu kuma ɗan takaran shugaban kasa ya janye masa idan aka zo zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.
Okorocha ya ce Tinubu babba ne, saboda haka zai tausa shi ya janye masa idan lokacin zaɓen fi dda gwani yayi
” Ni da Tinubu ne za mu kasance a kan gaba a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa a APC. Amma kuma a lokacin zan tausa shi ya ci girma ya janye ya bar mini wurin ni in kwafsa da PDP.
” Ni mutum ne mai tausayin jama’a, bana yin ƙabilanci. Musulmi ne kai, Kirista ne kai, Bahaushe, Inyamiri ko bayarabe, ni a wurina mutim kawai nake gani. Babu banbancin addini ko na kabila
Okorocha ya kara da cewa, shine ya ke tada kura a yqnkin kasar Igbo haka kuma shima Tinubu ne ke tada kura a yankin kasar Yarabawa. A dalilin haka kuwa su biyun ne za a fafata da su idan zaɓe ya zo.
A ƙarshe ya roki ƴaƴan jam’iyyar su kakkaɓe katin zaben su kowa ya kwana ya kum tashi da shirin tunkarar babban zaɓe da ke zuwa.
” Kada ka saida ƴancinka, a tabbata ka yi zabe domin kanka da cigaban kasa Najeriya.