Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ta kusa durƙushewa, saboda haka ba ta bukatar komai a yanzu, sai gwarzon namijin da zai ceto ta ya ceto al’ummar ƙasar nan.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka damƙa masa fam na neman takarar shugaban ƙasa, wanda wata ƙungiya ta sai masa.
Tambuwal ya ce wata ƙungiya ce mai suna Concerned Citizen of Nigeria ta sai masa fam ɗin.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Tambuwal mai suna Muhammad Bello ya sa wa hannu kuma ya aika wa manema labarai, Tambuwal ya ce shi da wasu sun fice daga APC saboda jam’iyyar ta kasa a kowane fanni.
Yayin da ya ke nuna damuwa a kan taɓarɓarewar tattalin arziki, matsalar tsaro, rashawa da cin hanci, tsadar rayuwa, rashin aikin yi, Tambuwal ya ce ba haka kawai don neman mulki ya fito takara ba, sai don ya ceto ƙasar nan daga gagarimar matsala ko matsalolin da su ka dabaibaye ta, suka kuma dabaibaye ‘yan ƙasar.
Tambuwal wanda ko a 2019 sai da ya fito takarar shugabancin Najeriya, inda Atiku Abubakar ya kayar da su a zaɓen fidda-gwani na PDP, ya ce “idan har aka bari APC ta sake kafa gwamnati a 2023, to lamarin ƙasar nan zai durƙushe baki ɗaya.
Idan za a iya tunawa, Tambuwal ya kwashi ‘yan kallo, yayin da ya ce kada a zaɓi wanda ya cimma shekaru 60 a zaɓen shugaban ƙasa.
Gwamna Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto da ke neman a tsaida shi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, ya gargaɗi ‘yan Najeriya cewa kada a yi saki-na-dafen sake zaɓen dattijon duk da ya cimma shekaru 60 abin da ya yi sama a matsayin shugaban ƙasa, a zaɓen 2023.
A yanzu dai Tambuwal shekarun sa 56 da haihuwa, kuma ya dage bakin ƙoƙarin sa ya na son ganin cewa PDP shi ta tsayar, ba Atiku Abubakar ko wani ba.
Tambuwal ya yi wannan bayani a Jihar Jigawa, bayan da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) na Jihohin Arewa 19 su ka yi masa mubaya’a, su ka ce shi ne ɗan takarar su.
Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Sokoto, Bashir Usman ne ya wakilci Tambuwal a taron.
“Matasan Najeriya su ke da ƙasar nan. Duk wanda ya haura shekaru 60 a duniya, shure-shuren ƙarasawa ya tarad da mahaliccin sa kawai ya ke yi amma ba motsa jikin ƙarin ƙarfin iya shugabancin ƙasa ya ke ba.” Inji Tambuwal a wurin taron.
“Mu na buƙatar shugaban ƙasar mai lafiya ƙalau. Mai ƙarfi gagau, mai kuzari garau. Kuma mai jimirin kazar-kazar da gwarin-guiwar jure gaganiyar shugabancin al’umma kamar Najeriya.
“Mu na buƙatar lafiyayyen shugaba wanda zai iya kewaye Najeriya ɗaya rana domin ya gani kuma ya ji dukkan abubuwan da ke faruwa ko su ke addabar ‘yan Najeriya. Amma ba wanda kawai zai zauna cikin ofis ya na shan iska ya na jiran a kawo masa rahotonnin da aka daddatse, aka cire wuraren da su ka kamata ya ji ba.”
Tambuwal kuma ya ce kada a zaɓi duk wanda aka san ya na fama da wata rashin lafiya wadda ya same ta ne saboda yawancin shekaru.