Wata fitacciyar mai gabatar da shirye-shirye a talbijin a ƙasar Ghana, Abena Korkor, ta bayyana cewa a dalilin neman mijin aure ta kwana da maza akalla 100 a tsawon rayuwanta zuwa yanzu.
” Neman mijin aure ya sa sai da na kwana da maza akalla 100 a tsawon rayuwata zuwa yanzu da nake da shekaru 32 a duniya. Amma har yanzu banyi aure ba.
Korkor ta ce haryanzu tana laluben mijin aure domin burinta shine ta yi aure ta haifi ƴaya.
Jaridar The Cable ce ta buga wannan labari inda ta kara da cewa Korkor ta ce ta taɓa zubar da ciki sau ɗaya.
” Na taɓa zubar da ciki sau ɗaya a rayuwa ta. Shima kuskure aka samu. Da wanda yayi min cikin ya ce baya so sai na zubar saboda ban su in tilastashi ya ga kamar da gangagar na kyale cikin don dole.