Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraniya ya jaddada cewa ya na so ya sasanta da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin ya tabbatar masa cewa Ukraniya ta fasa shiga ƙungiyar NATO, inda ita Rasha ɗin daga nan sai ta janye sojojin ta daga Ukraniya, kuma ta yi wa Ukraniya ɗin alƙawarin daina afka mata da yaƙi.
A ranar Litinin ne tsakar dare Zelenskyy ya yi wannan sanarwar , wadda a bisa dukkan alamu ta na nufin nan gaba kaɗan za a daina yaƙin, idan ɓangarorin biyu su ka amince.
“Wannan magana ce da ta shafi kowa da kowa, tunda dai Turawan Yamma sun kai mu sun baro, sun nuna ba ‘yan amana ba ne. Ukraniya kuma na buƙatar Rasha ta tabbatar mata cewa ba za ta mamaye ta ba nan gaba. Sannan ita ma Rasha mun tabbatar mata ba za mu shiga NATO ba, tunda ba ta son NATO kusa da ƙasar ta, ba ta ma son NATO ta ci gaba da faɗaɗa a yankin ta.” Inji Zelenskyy.
Ya ƙara da cewa da zaran an tsaida yaƙi kowa ya fahimci kowa, to zai zauna da Shugaba Putin domin tattauna yankin Crimea da Donbas, yankunan da ‘yan awaren da Rasha ke goyon baya su ke mulki.
A ranar Litinin kafin wannan jawabi sai da Zelenskyy ya bayyana cewa a shirye ya ke ya gana da Putin domin Putin ya fahimci matsayin sa.
Dama tun a makon jiya Zelenskyy ya shaida wa Ukraniyawa cewa su haƙura da mafarkin shiga NATO.
Wannan jarida a lokacin ta buga labarin Cewa Ukraniya ta janye tunanin shiga ƙungiyar NATO -Zelensky, Shugaban Ukraniya.
Shugaban Ukraniya Zelensky ya bayyana cewa Ukraniya ta haƙura da shiga ƙungiyar ƙawancen Sojojin Taron Dangi na Turai da Amurka, wato NATO.
Zelensky ya yi wannan bayanin ne ga tawagar wasu manyan jami’an Birtaniya a ranar Talata.
Ya shaida masa cewa da daɗewa an bai wa Ukraniya ƙofar shiga NATO a buɗe, to amma dai a yanzu shigar ba abu ne mai wuya ba. “Don haka Ukraniya ta haƙura.”
Dama dai shiga ƙungiyar NATO da Ukraniya ta yi niyyar yi, na ɗaya daga cikin dalilan da Rasha ta kai mata mamaya.
A na ta ɓangaren, Amurka ta ce za ta tallafa wa Ukraniya da dala biliyan 13.6 duk shekara, domin ta farfaɗo daga ɓarnar da Rasha ta yi mata.
Sannan kuma duk da ana ci gaba da kai harin mamaya, har yau ana kuma tattaunawa kan teburin shawara.
A makon jiya ne Premium Times Hausa ta buga labarin cewa Ukraniya ta ce NATO ta yi mata Ingiza-mai-kantu-ruwa, bayan da NATO ta ƙi tare mata faɗa da Rasha.
‘Ƙasashen NATO Sun Yi Min Ingiza-mai-kantu-ruwa, Sun Bar Mu Rasha Na Kwankwatsar Mu’ -Shugaban Ukraniya:
Shugaban Ukraniya Volodymyr Zelenskyy ya ragargaji Ƙungiyar Ƙasashen Ƙawance Dakarun Yaƙi ta NATO saboda sun ƙi yarda su haramta wa jiragen yaƙin Rasha giftawa cikin ƙasar sa.
Volodymyr Zelenskyy ya ce ƙin shata wannan gargaɗin ya sa Rashawa na samun galaba sosai a kan ƙasar ta. Haka dai Gidan Talabijin na Aljazeera ya ruwaito.
“Ai shikenan mun bani. A yau sojojin Rasha sun samu damar ragargazar birane, garuruwa da ƙauyukan Ukraniya, saboda NATO ta ƙi kafa dokar haramta jiragen Rasha giftawa cikin Ukraniya.” Haka Volodymyr Zelenskyy ya bayyana a cikin talbijin a ranar Juma’a.
“A yau NATO ta nuna ba ta da ƙarfi. Ta nuna gazawa, ta ruɗe kuma gigitatta ce. Ƙungiya ce wadda ba ta maida yaƙin ƙasashen Turai da ‘yancin Turai muradin ta mafi muhimmanci ba.”
“Dukkan waɗanda aka kashe dalilin wannan yaƙi, an kashe su ne saboda gazawar NATO da rashin haɗin kan ƙasashen da ke cikin ƙungiyar.”
Rasha ta amince ta tsagaita wutar yini ɗaya, domin kwashe mutanen da ke biranen Mariupol da Volnovakha da ta hana shiga da fita.
Rasha ta amince da tsagaita wutar yini guda domin a gaggauta kwashe ɗimbin mutanen da ke cikin garuruwan Mariupol da Volnovakha, garuruwa biyu da ta yi wa ƙofar-raggo.
Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce ta amince da tsagaita wuta domin a samu damar tura kayan agajin gaggawa da ɗimbin jama’ar da yaƙin ya ritsa da su a biranen biyu.
“A yau 5 Ga Maris, mun tsagaita wuta daga ƙarfe 10 agogon Moscow domin a samu shigar da kayan agaji da kuma kwashe mutanen da ke ciki Mariupol da Volnovakha.”
Amma dai har yanzu ba a ji komai daga ɓangaren Ukraniya ba. Sannan kuma ba a san ko har zuwa wane lokaci ne tsagaita wutar zai ɗauka ba. Duk da dai wani jami’i ya shaida cewa tsagaita wutar zai ƙare ne daga 4 na yamma.
Shi ma Magajin Garin Volnovakha mai suna Vadym Boychenko, ya ce, “ba mu da wani zaɓi sai ficewa daga garin.”
“Ai mutane su ne gari, ba gine-gine ko gidaje ba. Shi ya sa za a kwashe jama’a domin tsira da rayukan su.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Rasha ke ci gaba da mamaye Ukraniya.
Labarin baya-bayan nan, shi ne wanda aka buga cewa, ‘Iliya Ɗanmaikarfi ya ƙwace tulunan makamashin nukiliyar Waldiman Birnin Ƙib.’
A ƙazamin yaƙin mamayar Ukraniya da ƙasar Rasha ke yi, lamarin da ya yi kama da labarin cikin littafin “Iliya Ɗanmaikarfi”, wanda aka bada labarin bayyanar wani ƙaƙƙarfan jarumi a Rasha, lamarin na neman maimaita kan sa a zahiri, inda yanzu haka dakarun Shugaba Vladimir Putin na Rasha su na ci gaba da ragargazar ƙasar Ukraniya.
A ranar Juma’a ce dakarun Rasha su ka ƙwace babbar tashar makamashin nukiliya na Ukraniya da ke yankin Zaporizlizhia, kuma su ka ƙwace yankin baki ɗaya.
Tashar makamashin nukiliya ta Ukraniya ita ce mafi girma a duk faɗin Turai baki ɗaya.
Shugaban Ukraniya Volodymyr Zelenskyy ya tabbatar da cewa yanzu tashar nukiliyar ta na hannun dakarun Rasha.
Sannan kuma ya yi tofin Allah-waddai ga Rasha, tare da yin iƙirarin cewa sojojin Rasha sun harba makamai a tashar.
“Rasha ta zama shaiɗaniyar ƙasar da a tarihin duniya ita ce ta fara harba makami a tashar nukiliya.” Inji Zelenskyy, tare da yin kira ga duniya cewa ya na buƙatar ɗaukin gaggawa.
Ranar Alhamis dama dakarun Rasha sun ƙwace garin Khersen mai mutum sama da 290,000, bayan sun kewaye garin ba shiga, ba fita, tsawon kwanaki uku.
Aljazeera ta ruwaito cewa sojojin na Rasha sun nausa gari mai arzikin tashoshin jiragen ruwa na Ukraniya, wato Mykollaine da ke bakin ‘Black Sea.’
Rasha na ci gaba da mamaye Ukraniya, tare da shan alwashin cewa ba za ta taɓa bari ƙasar Amurka da Turawan Yamma su ƙulla ƙawancen girke muggan makamai a Ukraniya, ƙasa mai maƙwabtaka da Rasha ba.