Dan takarar shugaban Kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya soke taron bikin zagayowar ranar haihuwar sa saboda mummunar harin jirgin kasa da yan ta’adda suka yi a Kaduna ranar Litinin.
Mummunar Harin Jirgin kasa
Wasu da ga cikin matafiyan da suka tsira daga harin ƴan ta’adda da suka kai wa jirgin kasa hari sun ce harin yayi munin gaske domin maharan dun kashe mutane da dama sannan sun sace mutane dayawan gaske.
Usman Mu’azu da ya tattauna da BBC Hausa ya ce maharan sun rika shiga cikin tarago ɗaya bayan ɗaya suna ɗiban mutane son ransu.
” Muna cikin tafiya kawai sai muka ji karar abu kamar bam ya tashi ya kuma girgiza jirgin, hakan na faruwa ba jimawa aka soma harbe-harbe.
Mu’azu ya ce ya ga gawawwaki da dama, kuma abin ya fi shafar mata, saboda shi kansa a kan idonunsa ya ga gawawwakin mata uku zuwa hudu da aka harba.
“An kwashe fasinjoji da dama sun soma harin ne daga taragon baya, sai suka rinka bi tarago-tarago suna kwashe mutane da kashe na kashewa.
“Tun da misalin karfe 8 na saura na dare abin ya faru ake ta musayar wuta har zuwa wajen 9 da rabi”.
Haka shi ma wani Fasinja Sani Ibrahim da ya kubuta ya ce ‘yan bindigar na bin kowane tarago suna haska mutane domin tantace na dauka.
Ya ce kusan babu taragon da basu shiga ba, da harbin mutanen da suka yi kokarin lalubo wayarsu da wani nau’i na abin haska wuri.
“‘Yan bindigar suna da yawa ba zan iya tantace yawansu ba, amma har matar da ke zaune kusa da ni sun kashe ta.
“Sun umarci kowa ya kwanta a kasa, kar a motsa haka wasu daga cikinmu suka rinka dabbara jan jiki a jirgin domin shiga tarago na gaba.
“Sun yi wa jirgin kawayan saboda sun zo da motarsu da suka rinka kwashe mutanen domin garkuwa da su, sun soma ne da taragon farko wanda su ne manyan kujeru.”
A karshe Sani ya ce da safiyar yau Talata ya samu komawa gida, amma ya shaidi yadda fasinjoji da dama suka shiga yanayi na galabaita ga jini ta ko ina.
Discussion about this post