Mazauna Kaduna sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da su ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar sakamakon mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai a cikin jirgin kasa ranar Litinin.
Jirgin ya taso ne da misalin karfe 6:00 na yamma daga Abuja, babban birnin Najeriya. kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ne aka kai hari a tsakanin al’ummar Katari da Rijana.
‘Yan ta’addan kuma ana kiransu da ‘yan bindiga a Najeriya, sun dasa bama-bamai a kan titin jirgin tare da ajiye shi kafin su yi harbin kan fasinjojin a lokacin da suke kokarin bude kofa.
Gwamnatin jihar Kaduna da kuma hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya sun tabbatar da faruwar harin.
Tuni dai hukumar ta NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja da Kaduna har sai an sanar da hakan kan lamarin.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru ba amma akwai rahotannin kafafen yada labarai cewa sama da mutane 970 ne ke cikin jirgin.
” Mu dai gwamnagti ta gaza. Akwai wanda na sani ba a ganshi ba har yanzu. Mun yi binciken amma shiru. ya dai kamata a ayyana ranakun musamman domin zamammakoki. In ji Sani Abdu.
Ummi Mohammed ta ce” Akwai ‘yar uwarta da mijinta da ba asan inda suke ba har yanzu. Gaba daya muna cikin zullumi da damuwa.
Alkali Sahfiu ya ce ” Ace wai daga Kaduna zuwa Abuja ya gagari gwamnatin Najeriya. Wannan lalacewa har ina tsakani da Allah. Ba titi ba ba jirgin kasa ba. Kai ta saman ma an kaiu mata hari a makon jiya. A gaskiya muna cikin tsananin damuwa da rudani yanzu haka.