Sanatocin Najeriya sun yi kira ga jami’an tsaro su riƙa tashi haiƙan su na hana mahara kashe jama’a, maimakon sai bayan an yi kisa sannan su fara yaƙi da ‘yan bindiga.
Sun ce ta haka ne kawai za a iya magance yawan kashe mutane da asarar ɗimbin dukiyoyin da ake yi sanadiyyar munanan hare-hare da farmaki da samamen da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankunan karkara.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ne ya yi kiran, bayan de Mataimakin Bulalar Majalisar Dattawa, Aliyu Abdullahi ya yi ƙorafin irin mummunan kisan da ‘yan bindiga su ka yi a garin Nasko cikin Ƙaramar Hukumar Magama.
Sanata Abdullahi ya ce maharan sun kutsa ne daga cikin Jihar Zamfara, su ka kai harin wanda su ka kashe Babban Jami’in ‘Yan Sanda na Yanki (DPO) da wasu mutanen garin da dama.
Duk da Omo-Agege ya jinjina wa jami’an tsaro saboda kai farmaki cikin gaggawa da su ka yi, har su ka kori ‘yan bindigar, amma kuma ya yi kira gare su su riƙa ɗaukar matakan gaggawa tun kafin mahara su kai ga yin kisa su na ƙone duniyoyi.
Omo-Agege ya ce zai fi kyau a ce jami’an tsaro su na hana ‘yan bindiga yin kisa da ɓarnata dukiyoyin al’umma.
“Daga bayanan da muka yi, mun fahimci jami’an tsaro sun yi ƙoƙari sosai wajen korar maharan, wannan ko tantama da tababa ba mu yi.
“Jami’an tsaro sun yi ƙoƙari sun koma inda su ka fatattaki mahara.
“Za mu so a ce sun ɗauki matakin fatattakar maharan tun kafin su kai ga kashe rayukan jama’a.
“Duk da haka dai za mu ci gaba da bai wa jami’an tsaro ƙwarin guiwa, ta yadda za su riƙa sa-ido sosai a yankunan ƙasar nan, musamman a Jihar Neja, jihar da kusan a sahun gaba ta ke a faɗin ƙasa fiye da sauran jihohi masu yawa.”
Daga nan sun yi shiru tsit na minti ɗaya, domin jimamin mutanen da ‘yan bindigar su ka kashe.
Discussion about this post