An shiga makonni ko wata biyu cur kenan ana fama da matsanancin ƙarancin fetur a Najeriya.
Mafi yawan gidajen mai sun rufe, kaɗan ne ke sayar da man su ma jifa-jifa, kuma inda ake sayarwar akwai dogon layi.
Ko dai ka saya da tsada a hannun ‘yan bumburutu, ko kuma ka ɓata lokaci ka sha da tsada, kuma da wahala a gidajen mai.
Ƙarin dagulewar al’amarin kuma shi ne yadda harkoki da dama su ka tsaya cak, saboda an dogara da fetur wajen gudanar da harkokin.
Tun farko dai Gwamnatin Tarayya ta ɗora laifin matsalar fetur ɗin kan yadda aka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium a cikin Najeriya, wanda ya lalata injinan dubun-bubatar motoci.
Duk da ana shan fetur aƙalla lita miliyan 1.6 kullum a Najeriya, har yau an kasa gyara matatun mai. Amma kuma a duk shekara sai sun cinye biliyoyin kuɗaɗe da sunan gyara ko kula da su.
Shin kamfanonin da suka shigo da gurɓataccen mai ne matsalar Najeriya, ko kuwa waɗanda ke da alhakin kula da harkokin fetur a Najeriya?
Ministan Fetur Kuma Shugaba Buhari:
Muhammadu Buhari shi ne Ministan Fetur, kuma Shugaban Ƙasa. Shi ne ke da alhaki ko bada umarnin duk wani tsari ko hukunci da aka yanke a ɓangaren fetur da ɗanyen mai.