Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta ƙaddamar da wani sabon shiri domin tallafa wa matasan da su ka ci moriyar shirin nan na N-Power domin su samu jarin shiga sana’ar aikin gona.
Shirin, wanda aka jima ana jiran sa, ma’aikatar za ta aiwatar da shi ne tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma waɗanda su ka ci moriyar kashi na ‘A’ da na ‘B’ na N-Power ne za su fara amfana da shi.
A wajen bikin ƙaddamar da shirin wanda aka yi a Cibiyar ‘Yan Jarida da ke Radio House a Abuja a ranar Litinin, an bayyana cewa daga cikin mutane 467,183 da aka horas, waɗanda kuma su ka nuna sha’awar shiga shirin, an zaɓi mutum 75,600 da za a fara yi wa bita wanda daga baya za a ba kowannen su rancen kuɗi har na naira miliyan 3 daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin ya ja jari idan an ga ya cancanta.
A wajen bikin ƙaddamarwar, ministar, wadda Babban Sakatare na ma’aikatar ya wakilta, wato Alhaji Bashir Nura Alƙali, ta gode wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari saboda ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi ba ji ba gani don rage fatara da yunwa a ƙasar nan da kuma tallafin da ta ke ci gaba da bai wa Tsare-tsaren Inganta Rayuwa na Ƙasa (NSIP).
Haka kuma ta taya mutane 467,183 da aka horas murna, wato waɗanda su ka nuna sha’awar shiga shirin mai suna NEXIT-CBN AGSMEIS daga cikin mutum 500,000 da aka yaye a kashi na ‘A’ da na ‘B’.
Hajiya Sadiya ta bayyana cewa wannan shi ne mataki na farko daga cikin sauran matakai daban-daban da za a gudanar a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).
Ta ce: “Buri na ne a ko yaushe in ga cewa ‘yan kashi na ‘A’ da na ‘B’ na shirin N-Power da aka yaye ba a bar su haka nan kara-zube ba. A wurare da dama, na sha bada tabbaci ga waɗannan ɗimbin matasa waɗanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta sha fama tare da Babban Bankin Nijeriya ta horas da su sun cimma wannan muradin.
“A yau an kawo gaɓar da za a soma cika burin kammala wannan bitar domin a bada dama ga waɗanda su ka ci moriyar shirin kuma su ka nuna sha’awar su ta shiga sabon tsarin tallafi wanda CBN ya kawo.
“Domin a samu sauƙin gudanarwa, za a aiwatar da wannan shirin bitar ne mataki-mataki. Bari kuma in shaida maku cewa dukkan jihohi 36 da yankin Abuja sun shiga cikin wannan shiri na NEXIT da aka daɗe ana jiran sa.
“Jimillar mutum 75,600 su ka shiga cikin wannan kashi na farko na horaswar. Za mu ci gaba da horas da sauran kashi-kashin nan ba da jimawa ba.
“Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta sadaukar da kan ta wajen tabbatar da cewa an cimna nasarar aiwatar da dukkan manyan shirye-shiryen da aka kawo don tallafa wa al’umma domin a cimma muradan da aka tsara.
“Shirin N-Power wani babban ɓangare ne na Tsare-Tsaren Inganta Rayuwa na Ƙasa waɗanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta ke gudanarwa da nufin cimma muradun ƙasa na rage fatara tare da samar da aikin yi.
“Shirin N-Power shi ne hanyar da za a bi a taimaki matasan Nijeriya su samu horarswar da za su gyara rayuwar su domin ganin sun kasance masu warware matsaloli kuma masu sana’ar kan su a cikin al’ummar su.”
A jawabin maraba da ya gabatar a taron, Babban Sakataren ma’aikatar, wanda Daraktan Tsare-Tsare, Bincike da Alƙaluma a ma’aikatar ya wakilta, wato Mista Raphael Oraeluno, ya hori masu cin moriyar shirin da su yi amfani da wannan dama da su ka samu da idon basira.
Ya ce: “Ina so in jaddada cewa tilas ne kowane mutum da aka horas ya kalli wannan dama ta musamman a matsayin wani alheri wanda ba zai banzatar da shi ba. Ku tuna da tafiyar da mu ka yi kafin mu zo wannan gaɓa. Kun fa samu wannan dama a ƙarshe. Ku maida hankali matuƙa a dukkan abin da za a koya maku a duk tsawon bitar da kuma bayan ta. A matsayin ku na masu cin moriyar shirin, za a ba ku dukkan horaswar da ku ke buƙata wanda zai ba ku garantin shiga cikin tsarin da CBN ya tanadar domin cimma wannan manufa.”
Shi ma Kodinetan Ƙasa na Tsare-Tsaren Inganta Ryuwa na Ƙasa (NSIP), Dakta Umar Bindir, ya shawarci masu cin moriyar da su yi amfani da tsarin na CBN kuma su zama masu dogara da kan su.
A ƙarshen bitar ta kwana biyar, za a ba masu cin moriyar, waɗanda su ka cancanta, rance har na naira miliyan 3 kowannen su kuma na wa’adin da bai haura shekara bakwai ba.