Na karanta wani rubutu da jaridarku mai albarka ta premium times ta ranar Alhamis, 24 ga watan Fabairun shekarar 2022 ta buga mai wannan take a sama wadda Alhaji Ahmed Ilallah Hadeja ya rubuta. Duk da ya ke marubucin ya fadi ra’ayinsane na k’ashin kansa, amma kama sunaye da yayi da kuma misalai da yayi k’ok’arin kawowa ya sa ya zama dole na yi wannan mukabalar ko ba don komai ba domin wayar da kan dubunnen masu karatu da kuma yiwa tarihi adalci
Da farko dai gaskiyar magana itace a matsayina na cikakken Bahadeje daga k’aramar hukumar Kafin-Hausa ni ban taba jin cewa akwai wani yanayi na wa raki ko banbanci da ake nuna min a cikin tafiyar siyasar Jihar Jigawa ba. Hasali ma, sai dai na ce idan aka kwatanta da wasu yankunan na Jigawa, toh mu Hadejiyawan ma ka iya cewa kusan munci rabonmu mun kuma fara shiga cikin na wasu
Zan koma tarihi domin bin daki daki na irin tagomashi da muka samu a wannnan yanki tun dawowar damokiradiyya a wannan kasa shekaru kusan ashirin da hudu da suka wuce
Jigawa dai kamar kowacce jiha ta kasu ne kashi uku a bisa kundin tsarin mulki na k’asa; wato Arewa ta tsakiya (masarautar Dutse), Arewa maso yamma (wato masarautun Gumel, da Kazaure da Ringim), da kuma Arewa maso gabas (wato masarautar Hadeja). Akwai kuma kashe kashe na tsarin masarautun gargajiyarmu ma su albarka na Dutse, da na Hadeja, da Gumel, da Kazaure da kuma Ringim guda biyar. Alhamdulillah mu mutanen Hadeja muna yiwa Allah SWT da kuma y’an uwanmu mutanen Jigawa godiya da cewa a kowanne tsagi mutum ya d’auko wannan rabe rabe na Jigawa mu kam kwalliya ta biya kud’in sabulu.
Mu dai Hadejiyawa sai son barka idan ka duba da yanayin cewa mu ke jan ragamar tattalin arzikin Jihar Jigawa wadda galibinsa na noma ne da kiwo da kuma kiwo da kamun kifi. Ga kuma albarka ta karatu da kuma shiga aikin gwamnati a tarayya da kuma jiha dayarjewar Allah SWT (a wasu bangarorin) y’an uwanmu na Jigawa.
Mu na da babban birnin masarauta na Hadeja wadda ba k’aramar habaka yayi ba da hanyoyi na zamani da makarantu manya da kuma asibitoci. Kuma babu ko da d’aya daga cikin manyan biranen mu guda bakwai na Auyo, Kafin Hausa, Kirikasamma, Birniwa, Guri, Kaugama da Mallam Madori da basu da kayatattun tituna, da manyan asibitoci, da fitilun titina kai harma da makarantar share fage na shiga Jami’a kai harma da Jami’a sukutun a cikin garina na Kafin-Hausa! Kai ko da garin Elleman da ke k’ark’ashin k’aramar hukumar Kaugama ba karamin birni ba ne idan za ka kwatantatashi da wasu garuruwan da ke wasu yankin.
Muna da hanyoyin mota na fita kunya da suka karade duk wani lungu da sak’o na wannan yanki da kuma katafaren aikin noma na Ma’aikatar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are wadda ya karade kananan hukomomi biyar daga cikin takwas da wannin yanki na mu mai albarka ya ke da su. Dad’in dad’awa, ubanmu, kuma shugabanmu wato mai Martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje Haruna CON shine Shugaban Majalissar Sarakuna na wannan Jiha tamu mai alfarma. Wannan tabbas ba k’aramar karramawa ba ce da d’aukacin y’an uwanmu na Jigawa su ka yi wa dukkanin wani Bahadeje da ransa ko bayan ransa.
Kai ko da a harkar siyasarma da rubutun Mallam Ilallah ya fi karkata, a cikin shekarun dai 24, wannan yanki ya fitar da Mataimakan Gwamna har guda hud’u, ministoci suma har guda hud’u,jakadodun kasanya(ambasadodi) kakakin majalissa na jiha, manya manyan sakatarori a jiha da kuma tarayya da kuma manya manyan muk’amai na nad’i da k’warewar aiki a gwamnatin tarayya.
Na san Ahmed Ilallah da masu tunani irin nasa za su iya cewa ai duk wannan tagomashin bai kai ga kujerar gwamna guda d’aya ba. Amsa ta garesu itace A’A. Domin kuwa, a yau zancen da ake na cewa akwai wad’anda su kafi kowa cancanta atakarar gwamna a kakar zaben na shekara ta 2023 uku, kusan uku daga cikinsu tsofoffine da kuma mataimakin gwamna mai ci a yanzu, d’aya daga cikinsu tsohon Minista ne, biyu daga cikinsu nad’ad’d’une a gwamnatin tarayya. Toh kun ga kuwa y’an uwana ai mai tafiya sama ya taka leda ai ya rage hanya. Domin kuwa akwai yankuna a cikin Jigawa da ba su da irin wannan tagomashi da Allah SWT da kuma y’an uwamnu al’ummar Jigawa su ka yi mana.
Na so a ce na yi wannan rubutun na gama ban kama suna ba, ba don cewa Mallam Illallah ya futo fili ya kama sunan tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma jagoran jama’iyyar PDP reshen jihar a cikin rubutunsa; wato Alhaji Dakta Sule Lamido (CON). Y’an magana na cewa gaskiya dai d’aya ce, daga k’inta sai bata. Hadeja ba ta samu wad’ancan tagomashe ba sai da Allah SWT mahallincin sammai da k’assai yayi amafani da wannan bawan Allah wajen tabbatar da hakan
Sule Lamido ya yi sanadiyyar nad’a marigayi Ambassador Daudu Suleiman daga k’asar Hadeja daga shekarar 1999 zuwa 2003 a matsayin babban jakadan Najeriya a babbar k’asar korea ta kudu. Ya kuma yi sanadiyyar zaman Ambassador Ahmed Abdulhamid Mallam Madori a matsayin Ministan gwamnatin tarayya daga 2005 zuwa 2007. Daga nan kuma Ambassador Mallam Madori ya zama wakilin Najeriya a babbar k’asar Turkiyya tun daga 2007 har zuwa 2015. Ga wadda ba su san harkar jakadanci ba, K’asashe irinsu Turkiyya da Korea ta Kudu sai d’an gata mai uwa a gindin murhun ke samun irin wannan wurare ko da a cikin jakadinmu. Sannan dai Sule Lamido ya sake yin sanadiyyar nad’a d’an sarki kuma jikan sarkin Hadeja, Alhaji Hassan Haruna a matsayin Minista daga 2007 har zuwa 2009.
Wani babban tagomashi ma shine, da Maigirma Sule Lamido yayi tunanin d’aga likafar matasan Jigawa domin haskasu a fad’in k’asa da ma duniya baki d’aya, ai cikinmu ya zo ya d’auko d’an mu mai hazak’a wadda kuma ba wai rasa irinsa akayi a sauran yankunan Jigawa ba wato Dakta Nuruddeen Muhammad ya yi masa Minista lokacin yana dan shekara 34 daga shekarar 2011 zuwa 2015. Kai koda Allah ya sa Dakta Nuruddeen ya bar gwamnati kafin wa’adin gwamnati ya k’are, ai y’ar mu ya d’auko y’ar yankinan wato Hajiya Hauwa Bello ‘yar shekara 40 ta maye gurbinsa. A yau dai irinsu Dakta Nuruddeen d’in sune dai hasken da mu mutanen Hadejan da mu ke ganin sun d’au hanyar da wataran ka iya kawo mana ita waccan kujerar da Ahmed Ilallah ya yi rubutu a kai. Kuma yadace a sani a lokacin da Hadeja take da wadannan mukamai amma yankin sa na Dutse babu ko minista ko ambasada ko daya kaga kenan Dakta Lamido ya baiwa Hadeja kulawa
Dakta Sule Lamido ya gina mana kwalejin share fagen shiga Jami’a da kuma Jami’a Sule Lamido duk a garin Kafin-Hausa. Ya gina mana Makarantar Koyar da Fasaha ta Bilyaminu Usman da ke Hadeja. Ya gina mana hanya mai tsawon kusan kilomita 160 daga Kanon dabo zuwa Hadeja. Wannan hanya dai ba sai na yi bayanin amfaninta na tattalin arzikin da zamantakewar wannan yanki ba. Ya mana hanya gangariya da ta had’a mu da babban birnin Jiharmu na Dutse. Ya futo da katafaren dajinnan na baturiya kan hanya tun daga kwanar arawa. Yayi hanya daga kwanar Auyo zuwa Kafin Hausa. Yayi tsohuwar hanya mai tarihi ta Hadeja zuwa Garun Gabas. Ya fara aikin hanyar Maigatari zuwa Diginsa har Birniwa. Ya gyara mana manyan makarantunmu ma su tarihi na gaba da sakandare. Ya d’aga likafar asibitocinmu zuwa manyan asibitoci. Uwa uba kuma ya karrama tare da martabawa da kuma mutunta masarautar mu mai daraja.
Wannan dai wasu kenan daga cikin tabbatattun ni’imomin da Allah SWT yayi amfani da Maigirma Tsohon Gwamna, kuma jagoran PDP na Jihar Jigawa wato Alhaji Sule Lamido ya kawo mana a wannan yanki namu. Menene ya kamata yayi? Sai mu godewa Allah SWT sannan kuma mu ci gaba da yi masa k’yak’yk’yawan zato da kuma taya shi da addu’a da kuma ci gaba da bashi dukkan wani goyon baya da zai iya buk’ata domin ci gaba da jagorancin al’umma cikin nasara da adalci.
Ita kujerar gwamna ai allurar cikin ruwace mai rabo kan d’auka. Abune wadda mutum d’aya ne kawai ka iya d’auka a kowanne lokaci. Kuma ikone da k’udura irin ta Allah mad’aukaki. Rashin ta a wannan yanki ba wai yana nufin domin wani laifi da mu ka yi wa Sule Lamido ne ko Badaru ba ballantana yazama laifin mutanen Jigawa. Lokaci ne na Allah, kuma duk lokacin da Allah SWT ya tabbatar da hakan babu wani mai hanawa.
Tabbas ne kamar yadda Mallam Ilallah ya fad’a a cikin rubutunn sa cewa mutanen kasar Hadeja kan iya k’in na su su so wani, kuma wannan daliline ya sa gaba d’aya su ka tattara kuri’unsu su ka ba Alhaji Ali Sa’ad daga Birnin Kudu a 1992; su ka tattara su ka ba Alhaji Saminu Ibrahim Turaki daga Kazaure a 1999 da kuma 2003; su ka sake tattarawa su ka ba Alhaji Sule Lamido a 2007 da 2011;haka kuma su ka sake tattarawa su ka ba Alhaji Badaru Abubakar Talamiz a 2015 da 2019. Saboda haka ina tabbacin cewa a cikin ikon Allah haka suma kafatanin y’an uwanmu na wad’ancan yankunan za su had’u wata rana su zabi mutumin wannan yankin a matsayin wadda zai jagoranci wannan Jihar.
Mu dai mutanen Jigawa dukkaninmu uwarmu d’aya ubanmu d’aya, yarenmu d’aya, addininmu d’aya, al’adarmu d’aya, sunayenmu iri d’aya, bukukuwanmu iri d’aya, yadda mu ke binne mamatanmu iri d’aya, arzik’inmu da talaucinmu iri d’aya, yanayin lafiya da jinyarmu iri d’aya, kuma hatta kamanninmu ma kusan irin d’aya ne. Shi sabani da zargi, da rashin jituwa da jefa maganganu ana samunsu a duk yanayin da zamantakewa ta haura mutane biyu, ballantana dubbai da miliyoyi. Zo mu zauna zo saba ne, kuma babu wata al’umma da duk halinta iri d’aya ne.
Akwai mutumin banza da na kirki a cikin kowacce al’umma. Haka kuma akwai mai kishi da akasin haka, a ko ina kamar yadda dole akwai mai fad’a da mai hak’uri ko girman kai da sauk’in kan. Kuma binciken masana kimiyya ta halayyar d’an Adam sun tabbatar da cewa wad’annan halaye kusan yawansu iri d’aya ne a cikin kowacce irin al’umma a duniya, ballantana dunk’ulalliyar al’umma irin ta mu ta Jigawa.
A k’arshe na ke son na cewa Mallam Ahmed Illalah cewa mu Hadejiyawa ba mu yadda da cewa y’an uwanmu na sauran yankunan Jigawa suna yi mana kallon wani zunubi na musamman ba. Zama ne idan yayi zama ko hak’ori da harshe hak’uri akeyi. Haka ma mata da mijinta. Ballantana mutum da y’an uwansa na kusa. Kafin azo zancen mutanen unguwa, zuwa kan gari da gunduma, da kuma yanki har ya zuwa Jiha ba ki d’aya. Jigawarmu dai itace abar alfaharinmu baki d’aya.
Adamu maibada shawara ga Dakta Sule Lamido akan watsa labarai ya rubuta daga garin Kafin-Hausa, Jihar Jigawa.