Gwamnatin Amurka ta isar da gargaɗi ga Chana cewa ta daina goyon bayan Rasha a yaƙin da ta ke yi da Ukraniya. Haka dai Gidan Radiyon BBC ya ruwaito.
BBC ya ce wani jami’in Amurka da ba a ambaci sunan sa ba ya shaida wa wasu kafafen yaɗa labarai cewa Rasha ta nemi taimakon kayan soja ga Chana a lokacin da ta fara mamayar Ukraniya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Chana ba ta maida raddin wannan zargi kai-tsaye ba, amma ta zargi Amurka ya barbaɗa ƙarairayi da sharri a kan Chana a duniya.
An yi wannan musayar yawun ce kafin ƙasashen biyu su yi taron ganawa a Rum, Italy.
Wasu rahotannin sun ce Rasha ta nemi ƙananan na’urori masu sarrafa kan su da kan su (drones), kuma wasu kayan yaƙi, kamar yadda wasu jami’an gwamnati a Washington su ka yi zargi.
Cikin wata hira da aka yi Mashawarcin Tsaron Amurka Jake Sullivan a CNN, ya ce Rasha da Chana na tattaunawa a asirce a Beijing. Kuma ya ce to idan Chana ta taimaki Rasha, za a ƙaƙaba mata takunkumin da za ta ɗauki shekaru masu tsawo ba a cire mata shi ba.
“Ba za mu bari Chana ta riƙa samar wa Rasha wani sauƙi daga takunkumin da aka ƙaƙaba mata ba ko wata ƙasa ko a duniya baki ɗaya.”
Sullivan ya ce “mun tabbata Chana ta na da cikakkiyar masaniyar cewa Rasha za ta mamaye Ukraniya, tun ma kafin ta mamaye ɗin.”
Amurka Makaryaciya Ce -Chana:
Kakakin Yaɗa Labaran Ma’aikatar Harkokin Wajen Chana mai suna Zhao Lijian ya ce Amurka tantangaryar makaryaciya ce, kuma tun da aka fara rikicin Rasha da Ukraniya Amurka ɗin ke yaɗa ƙarairayi da sharri da kitsa tuggu a kan Chana.