Majalisar Dattawa ta amince cewa a bai wa dukkan ƙananan hukumomin Najeriya baki ɗaya da ɓangaren shari’a ‘yancin cin gashin kan su.
Amincewa da hakan ya biyo bayan kaɗa ƙuri’ar da aka yi kan Rahoton Kwamitin Sake Nazarin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kan ƙudirin 2022 a zaman majalisar na ranar Talata.
Yayin zaɓen dai sanatoci 92 sun goyi bayan ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 da kuma kotunan jihohi. Sai dai an samu sanatoci biyu da ba su goyi bayan bayar da ‘yancin cin gashin kai ɗin ba.
Haka kuma Sanatoci 83 sun goyi bayan a bai wa ƙananan hukumomin ‘yancin gashin kai. Sanata ɗaya ne kaɗai ne bai goyi da bayan hakan ba.
Haka kuma Sanatocin ba su goyi bayan kafa dokar bayar da fansho ga shugabannin majalisun Dattawa da na Tarayya.
Sanatoci 53 ne ba su goyi baya, inda 34 suka goyi baya. Sun kuma yi fatali da wasu ƙudirorin tilasta kafa doka, ko da Shugaban Ƙasa ya sa ƙafa ya take ƙudirorin don kada su zama doka.
Sun ƙi amincewa da ƙudirin neman canja sunan Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a cikin Jihar Filato zuwa ƙaramar hukumar “Gwoll”.