A Lura: Duk ƙudirin da Majalisar Dattawa ta amince da shi, idan Majalisar Tarayya ba ta amince ba, to za a jefa shi a kwandon shara.
Haka duk ƙudiri ko gyaran dokar da Majalisar Tarayya ta amince da shi, amma Majalisar Dattawa ba ta amince da shi ba, shi ma a kwandon shara ake jefa shi.
1. An Amince Da: Kudirin bai wa Ƙananan Hukumomi 774 ‘yancin cin gashin kan karɓar kuɗaɗen su kai tsaye.
2. An Amince Da: Ƙudirin bai wa Ƙananan Hukumomi ‘yancin tafiyar da mulki, ba tare da katsalandan daga gwamnatin jiha ba.
3. An Amince Da: Ƙudirin a canja sunayen Ƙaramar Hukumar Afikpo ta Arewa da Afikpo ta Kudu, cikin Jihar Ebonyi.
4. An Amince Cewa: A canja sunan Ƙaramar Hukumar Ƙunchi ta Jihar Kano.
5. An Amince Za A: Canja sunan Ƙaramar Hukumar Egbado ta Arewa da Egbado ta Kudu a Jihar Ogun.
6. An Yi Fatali Da: Kudirin neman a canja sunan Karamar Hukumar Barikin Ladi ta Jihar Filato
7. An Amince Da: Ƙudirin neman a gyara sunan Ƙaramar Hukumar Atigbo ta Jihar Oyo.
8. An Yarda Da: Ƙudirin neman a gyara sunayen Ƙaramar Hukumar Obia/Akpor cikin Jihar Ribas.
Discussion about this post