Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken kuɗaɗen da aka rasa masu su, ya ce ya bankaɗo naira biliyan 300 da aka kimshe a bankuna daban-daban.
Kwamitin ya bayyana haka a ranar Laraba, lokacin da manyan jami’an wasu bankuna su ka bayyana gaban kwamitin domin amsa wasu tambayoyi.
Kwamitin wanda Honarabul Uyime Idem, ɗan PDP daga Akwa Ibom ke shugabanci, an ɗora masa aikin binciko “kuɗaɗen da aka sace a aka kimshe a bankuna, kuma aka rasa masu kuɗaɗen waɗanda ke kimshe a cikin bankuna. Cikin kuɗaɗen kuwa har da kuɗaɗen somin-taɓin kwangiloli da gwamnati ke bai wa kamfanonin masu kwangila.”
Wani aikin da aka ɗora wa kwamitin kuma shi ne gano gargadar bambancin lissafi ko baddala alƙaluman ƙididdiga da aka yi zargi a Babban Bankin Najeriya, CBN.
Idem ya ce zuwa yanzu dai kwamitin ya bankaɗo naira biliyan 300, kuma ya na kan hanyar bankaɗo sama da naira tiriliyan 1.3.
“Zuwa yanzu dai mun bankaɗo kimanin naira biliyan 300 da aka kimshe a bankuna daban-daban. Kuma na tabbata zuwa lokacin da za mu kammala wannan gagarimin aiki, kuɗin da za mu bankaɗo sai sun haura adadin waɗanda Majalisa ta ce mu bankaɗo.
Idem ya ƙara da cewa Bankin Citi Bank na da bashin naira biliyan 99 na Gwamnatin Tarayya.
Sai dai kuma manyan jami’an bankin ba su amince da wannan adadin da Kwamitin Majalisar Tarayya ya bayyana ba.
Babban Daraktan Ayyuka na Citi Bank, Ngizi Omoke-Eyi, ta ce bankin na da asusu bakwai kaɗai, kuma wanda ya fi kuɗaɗe a cikin su ma dala 203,000 kaɗai ne a cikin sa. Sauran kuɗaɗen wasu ‘yan nairori ne ba masu yawa ba. Kai ashe ma na yi kuskure, nairori ne kuɗaɗen ba dala ba. Asusu biyar ne, kuma ko lambar rajistar BVN ba su ma da su.”
Ɗan Majalisar Tarayya Afolabi Olamilekan daga Osun ya zargi Citi Bank da ɗibga mummunan laifin sauya kwafe-kwafen takardun bayanan da suka bai wa kwamitin da farko.
Daga nan sai ya nemi a gabatar da ƙudirin umartar Omoke-Eyi cewa ta yi rantsuwa.
“Akwai buƙatar mu ɗora su kan sikelin rantsuwa. Domin abin da su ke yi mumnunan laifi ne. Saboda su na son ba mu wasu adadi ne daban da wanda su ka ba mu tun da farko.” Inji Olamilekan.
Yayin da ya ke bayyana yadda kuɗaɗen su ka kai har naira biliyan 99, Idem ya ce kwamitin sa ya haɗa adadin kuɗaɗen da ke cikin dukkan asusun da ba su da lambar BVN ɗin bankin.
Bayan an yi doguwar taƙaddama, an amince wakilan bankin su zauna da jami’an tuntuɓa masu yi wa kwamitin bincike domin su ga komai ƙuru-ƙuru.
Baya ga Citi Bank, an gano akwai Naira biliyan 5.2 rataye a Hukumar Bunƙasa Hada-hadar Hannayen Jari ta Najeriya (NIPC).
Discussion about this post