Ƙungiyoyin mata daban-daban na Najeriya sun bai wa Majalisar Tarayya wa’adin kwanaki bakwai cewa su amince da Ƙudirin Gyaran Dokar Jinsi guda biyar, wadda makonnin baya su ka yi watsi da su.
Matan sun yi wannan kiran ne a wani Babban Taron Manema Labarai da su ka yi a Abuja, bayan sun dakatar da zanga-zangar da su ke yi a kullum bakin ƙofar shiga ginin Majalisa a Abuja.
A farkon watan Maris ne Majalisa ƙi amincewa da yi wa Dokar Jinsi wasu gyare-gyare guda biyar da aka gabatar a majalisa, waɗanda za su gyara kiki-kaka ɗin da ke damun mata a cikin dokokin Najeriya.
Tun daga washegarin yi fatali da ƙudirin ne ƙungiyoyin mata daban-daban su ka riƙa yin zanga-zangar zaman dirshan a ƙofar shiga Majalisa, har tsawon kwanaki 10 na zaman majalisa.
Matan su na neman ko ana ha-maza-ha-mata sai an amince da ƙudirin, an yi wa dokakin biyar kwaskwarima.
Matan sun mamaye ƙofar majalisa su na zanga-zangar da su ka sa wa suna #nigerianWomenOccupyNass, a ƙarƙashin tushen WOMANIFESTO’, waɗanda gamayyar ƙungiyoyin mata ne na ƙasa da kuma na jihohi.
Duk da cewa Majalisar Dattawa ta tura masu tawagar sanatoci sun yi masu bayani, har yanzu babu wani mataki da aka ɗauka.
Amma kuma Majalisar Tarayya ta lashe aman ta, ta amince a yi wa dokokin jinsin waɗanda su ka shafi mata har guda uku daga cikin biyar ɗin kwaskwarima.
Zanga-zangar Ha-maza-ha-mata A Majalisa:
Matan sun ci gaba da zanga-zanga, inda a ranar 22 Ga Maris su ka yi nasarar kutsawa a cikin Majalisa, lamarin da hakan ya sa tilas Majalisar Tarayya ta turo wakilai bisa jagorancin Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa ya yi wa masu zanga-zangar jawabi. Daga nan ya roƙi masu zanga-zangar su bai wa majalisa lokaci ta bibiyi ƙudirorin. Hakan ne ya kawo dakatar da zanga-zangar.
Daga nan ne matan su ka yi taron manema labarai a ranar Laraba, inda su ka bai wa majalisa wa’adin kwanaki bakwai.
“Mun haƙura da zanga-zangar ce amma dakatawa ce muka yi, ba dainawa ba. Mun dakata ne don mu ba su lokaci kamar yadda su ka yi alƙawarin, mu ga ko za su cika alƙawarin? Waɗannan ƙudirorin gyaran dokar jinsi abu ne da zai kawo bunƙasar ci gaba a Najeriya.” Inji Abiodun Akiyode-Afolabi, a mamadin ƙungiyoyin matan.
Matan sun ce idan ba a cika masu alƙawarin ba kuwa, za su koma ci gaba da zanga-zanga.
Daga cikin ƙudirorin akwai gyaran dokar sashe na 26 na Tsarin Mulkin 1999, wadda su ke so a bai wa mijin ‘yar Najeriya da ba ɗan ƙasa ba, a ba shi iznin zama ɗan ƙasa.
Akwai kuma sashe na 31 da na 32(1), na Tsarin Mulkin 1999 da su ke so a yi wa kwaskwarima a bai wa mata dama zama cikakkiyar ‘yar asalin jihar da mijin ta ya ke, matsawar su ka cika cika shekara biyar abin da ya yi sama tare da mijin.
Sai na uku shi ne su na so a gyara sashe na 223 na Dokar Najeriya, ta yadda za a gyara dokar a riƙa naɗa mata kashi 35 bisa 100 muƙaman siyasa a cikin gwamnati.
Su na so a gyara Sashe na 147 da na 192 na Dokar naɗa Ministoci da Kwamishinoni, ta yadda za a riƙa naɗa mata ministoci kashi 35 bisa 100, su ma kwamishinonin su kasance kashi 35 bisa 100 mata ne.
Na biyar su na so a gyara sashe na 48, 49 da 91 na tsarin mulki, domin a riƙa zaɓen mata 37, 74 da 108 a Majalisar Dattwa, Majalisar Tarayya da Majalisun Jihohi.
Discussion about this post