Jami’an EFCC sun ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano cancak daga ofishin su na Shiyyar Legas zuwa Hedikwatar EFCC ta Abuja domin ci gaba da sharara masa tambayoyin salwantar maƙudan kuɗaɗe a lokacin mulkin sa.
Obiano zai sha tambayoyi bayan kuma an sharara wa matar da Misis Obiano mari a gaban jama’a, yayin da su ke miƙa mulki ga sabon Gwamnan Anambra, Charles Soludo.
EFCC ta kama Obiano a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan ya miƙa mulki a Enugu.
Ya garzaya Legas ne da nufin hawa jirgin sama zuwa Jihar Houston a Amurka, inda jirgi ke jiran sa.
Wannan rana ta zama baƙar rana ga Obiano, wanda a gaban sa kuma a gaban dubban jama’a, Bianca Ojukwu ta gaggaura wa matar sa mari wurin miƙa mulki.
Majiyar EFCC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an damƙe Obiano wajen ƙarfe 8:30 na dare a ranar Laraba, kuma washegari Alhamis aka ɗauko shi a jirgi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.
Har yanzu dai ba a san takamaiman ko naira biliyan nawa EFCC ke ƙoƙarin ganin Obiano ya amayas ba.
Sai dai kuma idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari ƙarshen 2021 cewa Hukumar EFCC ta rubuta wa Hukumar Shige da Fice Wasiƙa a ranar 15 Ga Nuwamba cewa su sa ido kan Obiano duk inda zai fita daga ƙasar nan. Su kula da ranar da zai fita ko ranar dawowar sa.
EFCC ta kama shi sa’o’i kaɗan bayan ya rasa rigar sulken kariya a lokacin ya na gwamna, rigar da ke hana duk irin ɓarnar da gwamna ya yi, ya fi ƙarfin kamu, sai dai a jira bayan saukar sa.