Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a karo ta biyu cikin shekara 8.
Kwankwaso ya aika da wasikar ficewa daga jam’iyyar ce rabar Talata inda ya aika da wasikar haka ga mazabar sa dake karamar hukumar Madobi jihar Kano.
Kwankwaso zai koma jam’iyya mai alamar kayan dadi, wato NNPP.
Kwankwaso ya bayyana wasu dalilai da suka sa ya fice daga PDP da suka hada da rashin jituwa tsakanin sa da jam’iyyar ta yankin Arewa Maso Yamma. Sannan kuma da ba a ga maciji tsakanin sa da Aminu Wali a jam’iyyar a Kano.
Abba Gida-Gida ya koma NNPP
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP a 2019, Abba Gida-Gida ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyya mai alamar kayan daɗi, NNPP.
Idan ba a manta ba Abba Gida-Gida ya faɗi zaben gwamna bayan kwabzawa da yayi da gwamna Abdullahi Ganduje da ya kusa kifar da shi badun Inkonkulusib da ya yi wa Ganduje rana ba.
Ana sa ran nan da kwanaki uku masu zuwa uban gidan sa tsohon gwamna, tsohon Sanata kuma tsohon Minista Rabiu Kwankwaso zai canja sheka zuwa jam’iyyar NNPP din.
A jawabin da yayi a mazabar sa a lokacin da yake bayyana ficewar sa daga PDP zuwa NNPP, Abba ya ce da jam’iyyar APC da PDP duk jirgi ɗaya ya kwaso su. Saboda haka ya ga cewa NNPC ce kawai makoma a garshi.
Rahotanni sun nuna cewa shima uban gidan sa Rabiu Kwankwaso zai bayyana komawarsa jam’iyyar NNPP ranar 30 ko 31 ga Maris kuma zai yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar.