Shugaban Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Ghebreyesus ya gargadi kasashen duniya da kada su sassauta sharuddan gujewa kamuwa da cutar korona domin har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa.
Ghebreyesus ya yi wannan gargaddi a garin Geneva ranar Laraba yana mai cewa yin gargadi ya zama dole ganin yadda cutar ke kara yaɗuwa a kasashen duniya.
Ya ce sassauta sharuddan gujewa kamuwa da cutar, yada labaran karya game da cutar, rashin yin allurar rigakafi na daga cikin dalilan da ya sa cutar ke kara yaduwa.
“Cutar ta sake barkewa a wasu kasashen duniya duk da cewa duniya gaba daya ta samu ragowa a yaduwar cutar.
“Dole a samu karuwa a yawan mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar idan har ana samun karuwa a yaduwar cutar.
Jami’ar WHO Maria Van Kerkhove ta ce bullowar zazzafar na’uin Omicron sannan da rikidan nau’in zuwa Omicron BA.1 da BA.2 na daga cikin dalilan da ya sa cutar ke ci gaba da yaduwa.
Ta kuma ce rashin kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar musamman amfani da takunkumin fuska, bada rata wajen tsayuwa kusa da mutane ya Kara yada cutar.
Maria ta yi kira ga mutane da kan yin allurar rigakafin cutar tare da neman ingantacen bayanai game da yaduwar cutar domin rashin samun bayanai ta gari game da cutar ya sa mutane ke kin kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.
Ta ce har yanzu cutar na nan sannan ba a kai matsayin da za a ce ga lokacin yanayi da cutar ya fi bullowa ba.