A ranar Juma’a ce Kotun Ƙoli ta jaddada soke rajistar wasu jam’iyyu 22 da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta yi.
Jam’iyyu 22 ɗin da aka soke rajistar su, su na daga cikin jam’iyyu 74 da INEC ta soke cikin 2020, bayan rashin ƙoƙarin su da kasa taɓuka samun ɗan zakara a matsayin kansila ko ɗan majalisa a zaɓukan baya da aka gudanar.
Cikin waɗanda aka maka kotu a ɗaukaka ƙarar da aka yi zuwa Kotun Ƙoli, har da Abubakar Malami, Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Tarayya.
Sunayen Jam’iyyun Da Aka Soke:
ACD, ANDP, ABP, AGAP, ASD, CAP, DPC, GPN, MMN, MPN.
Sauran sun haɗa da NGPA, NFD, PCP, PPA, PDC, YDP, RBNP, SNC, SPN, UDP, UP da WTPN.
Bayan INEC ta soke rajistar su cikin 2020, sun ɗaukaka ƙara, inda su ka yi nasara, amma kuma INEC tai ƙara Kotun Ƙoli inda ta yi nasarar.
Da ake yanke hukunci a ranar Juma’a, ɗaya daga cikin alƙalan mai suna Ejembi Eko, ya jingine hukuncin da Kotun Daukaka Ƙara da ke Abuja.
“A yau Kotun Ƙoli ta jaddada hukuncin da INEC ta ɗauka, wanda ta soke rajistar jam’iyyun siyasa 22, waɗanda Kotun Ɗaukaka Ƙara su ka maida wa rajistar su.
Idan ba a manta ba, a ranar 6 Ga Fabrairu, 2020 INEC ta soke rajistar jam’iyyu 74 waɗanda ta ce sun kasa nasara a zaɓukan baya, ko da kuwa ta muƙamin siyasa ko ɗaya.